Cikakken rahotu: Majalisar dokokin Najeriya ta tafi hutu ta bar baya da kura kan kudurori


Bisa dukkan alamu matakin amincewa da wasu muhimman kudurorin dokoki da `yan majalisun dokokin Najeriya suka yi ya bar baya da kura, kasancewar babbar jam`iyyar hamayyar kasar, wato PDP ta ce za ta kalubalanci wasu kudurori biyu. Kudurorin na da matukar muhimmanci ga tattalin arziki da kuma dimokuradiyyar kasar.

Wannan na faruwa ne yayin da 'yan majalisar suka fara hutunsu na shekara-shekara.

A makon jiya ne `yan majalisar dattawa da ta wakilai suka amince da kudurin gyara ga dokar zabe a wani yanayi mai takaddama, saboda `yan PDP sun ce sai an sanya batun amfani da laturoni wajen kada kuri`a da kuma sanar da sakamakon zabe.

Kudurin da bangarori biyu na majalisar suka amince da shi bai tanadi cewa dole a yi amfani da na'urar kwamfyuta wajen kada kuri'a da kuma aikewa da sakamakon zabe zuwa cibiyar tattara sakamako ba.

Haka nan majalisun sun amince da kudurin yin garambawul ga harkar man fetur wanda shi ma wasu 'yan PDP ke nuna tirjiya a kai - suna neman a kara kudaden da kamfanoni za su dinga kebe wa al`umomin da ake hakar mai a yankunansu zuwa kashi bakwai cikin dari na jarin kamfanonin, amma majalisun suka yi watsi da wannan bukatar.

Majalisun dai sun amince da a rika kebe kashi uku cikin dari ne ga al'umomin a sabuwar dokar, wanda ke nufin an yi wa al'umomin karin rabin kashi daya a kan adadin da aka saba ware masu.

''PDP Za ta kai kara kotu''

Secondus PDP
Bayanan hoto, Shugaban PDP Uche Secondus

To sai dai duk da cewa Majalisar Dokokin ta kasa ta amince da kududorin biyu ta hanyar kada kuri'a tsakanin 'yan majalisar, bisa dukkan alamu jam'iyyar PDP mai hamayya ba ta gamsu da matakin bangarori biyu na majalisar ba.

Sakamakon rashin gamsuwar, jam'iyyar PDP ta ce zata kalubalanci matakin a kotu.

Jam'iyyar APC mai mulki ce dai ke da rinjayen wakilai a cikin bangarorin biyu na majalisa - wato Majalisar Wakilai ta Tarayya da kuma Majalisar Dattawa.

Kafofin labarai a Najeriya sun ambato shugaban babbar jam'iyyar hamayya ta PDP na kasa, Mr Uche Secondus, na cewa yadda majalisar wakilai da ta dattawa suka ki amincewa a sanya shadarar doka da zata wajabta aikewa da sakamakon zabe zuwa cibiyar tattara sakamako ta hanyar amfani da laturoni, wata alama ce ta yadda jam'iyyar APC ''ba ta da niyyar karfafa dimokuradiyyar Najeriya.''

Jam'iyyar PDP ta ce tabbatar da zabe nagari, cikin 'yan ci da kamanta adalci, shi ne gimshikin dimokuradiyya. Shugaban nata Uche Secondus ya bayyyana cewa ''PDP zata dauki dukkan matakan shari'a da suka wajaba'' domin ganin matakin 'yan jam'iyyar APC a majalisar bai tabbata ba.

Tun farko dai babbar jam'iyyar hamayyar ta ce bata goyon bayan wasu sassa na shi ma kudurin dokar yi wa harkar man fetur a Najeriya garambawul, musamman yadda majalisar dokokin ta kasa ta amince da 3% a matsayin kason da za a rika kebe wa al'umomin da ake hako man fetur a yankunansu. Jam'iyyar PDP da kuma wasu gwamnonin kudancin Najeriya na ganin kamata ya yi adadin kason ya rubanya hakan.

'Yan Jam'iyyar APC sun yi wa PDP raddi

Abdullahi Adamu
Bayanan hoto, Sanata Abdullahi Adamu

Kawo yanzu dai babu tabbas kan lokacin da jam'iyyar ta PDP za ta shigar da kara, da kuma irin hujjoji da zata gabatar a gaban kotu. To amma bisa dukkan alamu lamarin na tayar da kura.

Sai dai 'yan jam'iyyar APC mai mulki na cewa babbar jam'iyar hamayyar na neman nade tabarmar kunya ne kawai domin kuwa tunda har majalisa ta riga ta amince da kudurorin, to batun zuwa kotu ba zai yi tasiri ba.

Sanata Abdullahi Adamu, dan majalisar dattawa daga jam'iyyar APC mai mulki ya ce ''sambatu'' kawai shuwagabanni na jam'iyyar PDP ke yi da nufin nuna wa talakawa masu goyon bayansu cewa wakilansu a majalisa ba su bayar da kai ba.

Sanata Abdullahi Adamu ya shaida wa BBC cewa ba su tsoron zuwa kotu domin ''kotu ta kowa ce'' kuma duk wanda ya ji an yi masa ba daidai ba na da 'yancin zuwa kotu. To amma ya ce a ganinsa lamarin kudurorin bai bar baya da kura ba.

Dan majalisar dattawan na jam'iyya mai mulki ya ce kamata ya yi 'yan PDP su hakura, su hada kai da sauran 'yan majalisa domin ciyar da kasa gaba - domin kuwa dama lamarin majalisa, batu ne na masu rinjaye ake amfani da ra'ayinsu.

Ya musanta zargin kumbiya-kumbiya da rashin nuna gaskiya wajen amincewa da kudurorin a majalisa, yana mai cewa an bi ka'ida.

Kawo yanzu dai abin da ya rage don kudurorin sun zamo cikakkun dokoki shi ne a mika wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kansu.

A cewar Abdullahi Adamu, abin da aka amince da shi a majalisa ya zauna kuma ''mai kwance wannan abu kawai sai Allah da ya yi mu.''

Kudurorin na da matukar muhimmanci ga makomar Najeriya

Wannan dambarwa tsakanin manyan jam'iyyun siyasar Najeriya dai ta bayyana karara tun lokacin da ake tafka muhawwara a cikin majalisa.

A wasu lokutan sai da aka bai wa hamata iska tsakanin 'yan majalisa sakamakon sabanin ra'ayi kan kudurorin.

Kudurorin dokokin guda biyu na daga cikin mafiya muhimmanci da majalisar dokokin ta kasa ta tafka muhawwara a kansu ta kuma amince da su cikin aikinta na tsawon shekaru.

Misali, shirin dokar yin garambawul ga harkar man fetur a Najeriya ya shafe fiye da shekaru goma a gaban majalisar, inda duk yunkurin da aka yi a baya na amince da shi ya faskara.

Tattalin arzikin Najeriya dai ya dogara ne kusan kacaukam kan albarkatun man fetur. Wannan ya sanya duk abinda ya shafi bangaren man fetur kan shafi kasar, da kuma janyo muhawwara tsakanin shuwagabanni da kuma talakawa.

Shi ma kudurin yi wa dokokin zabe gyaran fuska na da muhimmanci ga makomar Najeriya ganin kasar na tunkarar muhimman manyan zabuka a 2023 - wato nan da kasa da shekaru biyu masu zuwa. Abin da wannan kuma ke nufi shi ne dokar zata yi tasiri kan tafiyar dimokuradiyyar kasar.

A cikin watan Satumba ne dai ake sa ran 'yan majalisar zasu kammala hutunsu kana su koma bakin aiki na zaman majalisa. Babu tabbas kan abin da zai kasance yayin da 'yan majalisar wakilan da 'yan majalisar dattawa suka dawo daga hutun.

Rahotun BBC

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN