Cikakken rahotu: Abu biyar da ke tsunduma 'yan Najeriya cikin fargaba


Najeriya na fama da tashe-tashen hankali daban-daban da suka shafi matsalar tsaro, daga satar mutane domin neman kudin fansa zuwa ayyukan masu 'yan tawaye da kuma aikata miyagun laifuka da kusan daukacin kasar ke fama da shi.

Wani babban mai sharhi kan sha'anin tsaro a yankin Sahel da ke aiki da cibiyar Tony Blair, Audu Bulama Bukarti, ya ce matsalar tsaron na yin barazana ga: "Mutane na rasa rayukansu a lokacin da aka kai hari, yayin da fatan da ake da shi na mulkin dimukradiyya ke dakushewa a kasar."

A lokacin da aka zabi Shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2015, ya yi alkawarin kare rayuwar 'yan Najeriya daga ayyukan masu tayar da kayar baya da bata-gari. Amma har yanzu da ya rage kasa da shekaru biyu ya kammala wa'adin mulkinsa na biyu, kasar ta tsunduma cikin matsalar tsaro fiye da shekara 10 da suka gabata.

Ana alakanta hakan da talauci da rashin aikin yi ƙara ta'azzara matsalar tsaron.

Rashin aiki ga matasa ya kai matakin kashi 32.5 cikin 100 a kasar kuma suna tsaka mai wuya sakamakon tabarbarewar tattalin arziki da aka dade ba a gani ba tun shekara 27 da suka gabata.

Akidar masu ikirarin jihadi

taswirar da ke nuna yankunan da hare-haren Boko Haram suka daidaita
Bayanan hoto,

Tasawirar da ke nuna yankunan da hare-haren Boko Haram suka ɗaiɗaita. Majiya: ACLED da Binciken BBC

Duk da ikirarin da ya yi a shekarar farko da kama aiki kan cewa an murkushe mayakan Boko Haram, a yanzu Shugaba Buhari ya amince gwamnatinsa ta gaza kawo karshen ayyukan ta'addanci a kasar wanda ya faro daga arewa maso gabashin Najeriya.

Hakika, Boko Haram na kara fadada ayyukanta a sassan kasar tare da amfani da bakin talaucin da ake fama da shi a Najeriya da sauran matsalolin tsaro wajen yada mummunar akidarsu.

Kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana, kafin karshen shekarar 2020, kungiyar Boko Haram ta kashe kusan mutum 350,000 tare da tilasta wa miliyoyi barin muhallansu.

Boko Haram ta ci gaba da kai munanan hari da kafa tutocinta tare da mulkar mutanen yankunan ta karfin tuwo. Tana sanya wa manoma haraji, da sayar musu dabbobi. Hatta kasuwar kifi da ta yi fice a yankin tafkin Chadi, ta dawo karkashin ikon kungiyar.

An yi jana'izar manoma 43 da Boko Haram ta yi wa yankan rago a Zabarmari, mai nisan kilo mita 20 daga birnin Maiduguri, Najeriya, ranar 29 ga watan Nuwamba 2020, a lokacin da suke aiki a gonakin shinkafa a kusa da kauyen Koshobe.

ASALIN HOTON,AFP

Bayanan hoto,

Gwamman manoma mayakan Boko Haram suka yi wa yankan rago a shekarar da ta gabata

Kalubalen ya yi kamari a yankunan da ba sa hannun gwamnati, wurare masu sarkakaiya waɗanda da ma ba a kula da su, lamarin da ya janyo kungiyoyi irin wadannan ke cin karensu babu babbaka kuma ba tare da tsoron komai ba.

A shekarun nan, bangaren Boko Hram da ya balle tare da yin mubaya'a ga kungiyar IS a yankin Afirka, sun samu karfi fiye da Boko Haram. Wadda a yanzu suke goga kafada ta fuskar ayyuka da kungiyar IS a yankin. Kokarin sojojin gwamnatin Najeriya bai yi wani tasiri ba ga dukkan kungiyoyin.

Rikici tsakanin manoma da makiyaya

Shekara da shekaru ana samun tashin hankali tsakanin Fulani makiyaya da manoma a Najeriya.

Rashin daidaito kan filayen noma da ruwa da batun kiwon zamani da kuma matsalar sauyin yanayi, na daga cikin abubuwan da ke haddasa rikicin, yayin da manoma kan niki gari har kudancin Najeriya domin yin kiwo.

Don haka an kashe dubban mutane sanadiyyar wannan tashin hankalin.

Taswirar da ta nuna yankunan da rikicin fulani makiyaya da manoma ya yi kamari a Najeriya
Bayanan hoto,

Tasawirar da ta nuna yankunan da rikicin Fulani makiyaya da manoma ya yi kamari a Najeriya. Majiya: ACLED da Binciken BBC

Jihar Binuwe da ke tsakiyar Najeriya, ta fi yawan wadanda aka kashe saboda hare-haren.

A baya-bayan nan, mutane 7 sun mutu lokacin da 'yan bindiga suka bude wuta a wani sansanin 'yan gudun hijira da rikicin ya raba da muhallansu. Wasu kuma na zargin Fulani da sace mutane domin neman kudin fansa.

Mohammed Akdeef, manomi ne da rikici ya raba da matsugunansu, ya na magana da mutane a ranar 21 ga watan Yuli 2019, a wani sansanin 'yan gudun hijira na Madinatu da ke tsohon birnin Maiduguri

ASALIN HOTON,AFP

Bayanan hoto,

Mohammed Akdeef na daga cikin maonoman da rikici ya raba da muhallansu

Tashin hankalin ya janyo wasu daga cikin gwamnonin jihohin haramta kiwon sake, abin da ya kai su takaddama da gwamnatin tarayya.

A shekarar 2019, gwamnatin kasar ta kaddamar da shirin sauya yi wa kiwon dabbobi garambawul na shekara 10, domin takaita yawo da dabbobi da bunkasa fannin kiwo da nufin kawo karshen tashin hankalin.

Sai dai masu sukar lamarin na cewa rashin shugabanci da kudade da tsaiko wajen aiwatar da shirin na yi wa lamarin kafar ungulu.

Matsalar 'yan bindiga da satar mutane

Daya daga cikin lamari mafi firgitarwa ga iyalai a Najeriya shi ne yawaitar sace daliban makaranta ko dai a azuzuwansu ko a ɗakin kwanansu.

An sace sama da dalibai 1,000 a makarantunsu daga watan Disambar 2020, wasu daga ciki an sako su bayan biyan fansar makudan kudade.

Yawancin masu sace mutanen ana yi musu lakabi da "'yan bindiga". Bata-garin na kai hare-hare kauyuka da sace mutane da kona musu gidaje.

Hare-haren 'yan bindiga ya tilasta wa dubban 'yan Najeriya tsere wa matsugunansu, inda suke fakewa a wasu sassan kasar. Yankin Arewa maso gabas ne wurin da lamarin ya fi munana.

A Jihar Zamfara kadai, an kashe sama da mutum 3,000 daga shekarar 2012, kuma har yanzu ana ci gaba da kai wadannan hare-hare.

An rushe daruruwan makarantu sakamakon sace daliban makarantu a jihohin Zamfara da Neja, inda cikin wadanda aka sace har da yara 'yan shekara 3.

Alamu sun nuna kasuwar sace mutane na kara fadada zuwa wasu sassan Najeriya, kuma lamarin kamar ya fi karfin sojojin kasar.

Hakan ya zama babbar barazana ga kasuwanci da ilimi da kuma uwa uba, fannin noma.

line

Tayar da kayar bayan 'yan aware

Kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (Ipob) sun sha fafatawa da jami'an tsaron Najeriya.

IPOB na son wasu jihohin kudu maso gabashin kasar, wanda yawancinsu 'yan kabilar Ibo ne su, hade wuri guda domin ballewa daga Najeriya tare da kafa kasar Biafra.

Wani mamba a kungiyar Ipob

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Bayanan hoto,

Shugaba Buhari ya sha alwashin murkuhse Ipob

A shekarar 2014 ne aka samar da kungiyar, wadda Nnamdi Kanu ya kafa - yanzu haka yana tsare a hannun jami'an tsaro kan zargin cin amanar kasa da aikata ta'addanci.

Kamen nasa babban koma baya ne ga fafutukar da kungiyar ke yi.

Batun kafa kasar Biafra ba sabon abu ba ne. Tun a shekarar 1967 shugabannin yankin suka ayyana shi matsayin mai cin gashin kai, lamarin da ya janyo yakin basasa da ya haddasa mutuwar sama da mutum miliyan ɗaya.

An zargi magoya bayan Nnamdi Kanu da kai munanan hare-hare kan ofisoshin gwamnati da gidajen yari da ofisoshin 'yan sanda da shugabannin al'umma.

Shugaba Buhari ya sha alwashin murkushe Ipob. A watan da ya gabata ya wallafa a shafinsa na Twiter cewa "za mu maya wa wadanda ke tayar da zaune tsaye martani da harshen da suka fi fahimta".

Shafin Twitter ya cire sakon, saboda karya dokokin shafin, bayan an yi ta sukar sakon na Buhari a shafukan sada zumunta. Lamarin ya kai Najeriya ta dakatar da aikin shafin a kasar.

Tsagerun man fetur

Tsagerun Naija Delta (MEND) kan hanyar kai hari kan sojojin Najeriya a yankin Naija Delta ranar 17 ga watan Satumba 2008

ASALIN HOTON,AFP

Bayanan hoto,

Tsageru dauke da muggan makamai sun sha kai hare-hare kan bututan mai tun farkon shekarar 2000

Matsalar rashin tsaro a yankin kudancin Najeriya mai arzikin mai ba bakon abu ba ne.

Babban yanki ne da ake fitar da mai a Najeriya, tsagerun yankin kuma sun dade suna son a dinga ba su kaso mai tsoka na kudin da ake samu.

Sun ce yawancin man da ake samu a kasar ya fito ne daga yankinsu, wanda ya lalata wa al'ummarsu muhalli kuma ya janyo da wuya manoma ke yin noma ko kamun kifi.

Shekara da shekaru, tsagerun ke matsa wa gwamnati lamba ta hanyar sace ma'aikatan kamfanonin mai da kai hari kan jami'an tsaro da bututan mai da ayyukan ababen more rayuwa.

Domin shawo kan wannan matsala, tsohon shugaban Najeriya marigayi Umaru Musa Yar'Adua ya kaddamar da shirin yin afuwa a 2009, wanda ya kawo karshen ayyukan tsagerun yankin na Niger Delta.

Sai dai kungiyoyin asiri, sun ci gaba da zama babbar barazanar tsaro a yankin, inda ake gargadi jami'an masana'antu ayyukan tsagerun na sake dawowa.

Rahotun BBC

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN