Cikakken jerin manyan jami'an 'yan sanda 24 da IGP ya tura wasu shiyyoyin Najeriya


Usman Alkali Baba, Sufeto-Janar na ’Yan sanda (IGP), ya ba da umarnin aikawa tare da sauyawa mataimakan Sufeto-Janar na 'Yan sanda 24 (AIGs) mukamai da kuma wuraren aiki na shiyyoyi.

A cewar wata sanarwa da Legit.ng ta samo a ranar Talata, 27 ga watan Yuli, ta bakin kakakin rundunar ‘yan sanda, CP Frank Mba, sauya wuraren aikin ya dace da sabuwar manufar ci gaban 'Yan Sandan Najeriya.

Sanarwar ta nuna cewa AIG Bala Ciroma zai koma shiyya ta 7 Abuja yayin da AIG Usman Belel, AIG John Amadi da AIG Adeleke Adeyinka aka tura su zuwa FCID Annex Lagos, Maritime da shiyya ta 9 da ke Umuahia bi da bi.

Jerin Jami'an 'Yan Sanda da IGP ya tura jihohin Najeriya baki daya


Ga jerin sunayensu:


AIG SPU FHQ Abuja - AI Zaki M. Ahmed

AIG Shiyya ta 4 Makurdi - AIG Mustapha Dandaura

AIG CTU FHQ Abuja - AIG Dansuki D. Galadanchi, mni

AIG Shiyya ta 17 Akure - AIG Okon Etim Ene, mni

AIG 'Yan Sintiri FHQ Abuja - AIG Usman D. Nagogo

AIG Shiyya ta 7 Abuja - AIG Bala Ciroma

AIG Shiyya ta 9 Umuahia - AIG Adeleke Adeyinka Bode

AIG Shiyya ta 13 Ukpo-Dunukofia Awka - AIG Muri Umar Musa

Kwamanda Polac Wudil-Kano - AIG Lawal Jimeta Tanko

AIG FCID Annex Lagos - AIG Usman AlHassan Belel

AIG DOPS FHQ Abuja - AIG Adebola Emmanuel Longe

AIG Sashen Zuba Jari FHQ Abuja - AIG Musa Adze, fdc

AIG DICT FHQ Abuja - AIG Philip Sule Maku, fdc

AIG Shiyya 6 Calabar - AIG Usman Sule Gomna

AIG Hadin gwiwa - AIG Adamu Usman

AIG Shiyya ta 3 Yola - AIG Daniel Sokari-Pedro, mni

AIG DTD FHQ Abuja - AIG Ahmed Mohammed Azare

AIG FCID Annex Kaduna - AIG Maigana Alhaji Sani

AIG Shiyya ta 12 Bauchi - AIG Audu Adamu Madaki

AIG Maritime Lagos - AIG John Ogbonnaya Amadi, mni

AIG Shiyya ta 8 Lokoja - AIG Ede Ayuba Ekpeji

AIG Armament FHQ Abuja - AIG Mohammed L. Bagega

AIG Shiyya ta 15 Maiduguri - AIG Bello Makwashi

AIG Bangaren ayyuka FHQ Abuja - AIG Balarabe Abubakar

Da Ɗumi-Ɗumi: Sarki Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya Ya Rasu a Kaduna

Manufar sauye-sauye da sabbin aikewar

Legit.ng ta tattaro cewa IGP Alkali Baba ya tabbatarwa da kasa cewa aikawar da sauya manyan jami’an 'yan sanda zai kara taimakawa wajen jagorantar sabon hangen nesan 'yan sanda a kasar.


Ya bayyana cewa wannan sabon tsarin na 'yan sanda, a tsakanin sauran abubuwa, an shirya shi ne domin inganta ayyukan 'yan sanda a duk fadin kasar da kuma magance barazanar tsaro a kasar.

A wani labarin, ‘Yan sanda a ranar Litinin sun fatattaki wasu mambobin kungiyar IPOB wadanda suka mamaye Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja don jin yadda za ta kaya a shari’ar Nnamdi Kanu, shugabansu.

Mambobin kungiyar da suka fusata sun mamaye kotun gabanin shari’ar tasa, inda wani rahoton The Cable ya ce tuni an kame wasu daga cikin mambobin na IPOB.

Eid-el-Kabir: Bidiyo ya nuna Buhari yana tafiya zuwa filin Idi a Daura yayin daama'a ke taya shi murna

‘Yan kungiyar IPOB din suna ta rera taken nuna goyon baya ga Kanu tare da neman a sake shi.

Biyu daga cikinsu sun sanya tufafin yahudawa. Wani mutum sanye da bakaken kaya harma yayi wa wasu manema labarai jawabi amma yayi magana ne da yaren Igbo, inji Daily Trust.

Source: Legit.ng

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN