Bidiyon yadda wani mutum ya farmaki shugaban kasar Mali da wuka a Masallacin Idi, da abin da ya faru


Wani faifen bidiyo ya bayyana yadda wani mutum ya kai wa shugaban kasar Mali farmaki da wuka a Masallacin Idi ranar Sallar Layya.

Shugaba Assimi Goita yana cikin sahu domin gudanar da Sallar Idi a Bamako babban birnin kasar Mali ranar Talata 20 ga watan Yuli, kafin wani mutum ya farmake shi da wuka.

Mai farmakin ya yi yunkurin caka wa shugaban kasar wuka amma shugaba Goita ya tsira.

Dramatic moment Mali

Nan take jami'an tsaron shugaban kasa suka ci karfin mahara guda biyu a cikin Masallacin, kuma suka kama su suka jefa su a cikin wata motar soji suka tafi da su. Yayin da sauran jami'an tsaro suka kewaye shugaban kasar kuma suka fice da shi daga Masallacin.

Kalli bidiyo yadda lamarin ya faru:

Previous Post Next Post