APC za ta fuskanci wata rigimar cikin gida kan yadda za a shirya zabuka a Jihohi 36


Babban rikici ya na jiran jam’iyyar APC mai mulki a game da yadda za a gudanar da zaben mazabu, kananan hukumomi, jiha, har zuwa na kasa.

Ana sauraron yadda za a gudanar da zabukan ba tare da akwai cikakkiyar rajistar ‘yan jam’iyya ba.

Punch ta bayyana cewa baya ga rigimar zabe, akwai rashin jitu wa a game da shirin da manyan jam’iyya suke yi na fito da wasu ‘yan takara.

Akwai matsala a rajistar da jam'iyyar APC ta ke da shi

A jihohi 19 ne kadai ake da cikakken rajistar ‘ya ‘yan jam’iyya, an taba rajistar duk sauran jihohin.

Shugabannin jam’iyyar suna kokarin kawo ‘yan takarar da ake so kowa ya mara wa baya ba tare da an yi zabe ba, amma wasu sun ki yarda da wannan.

Jaridar ta ke cewa ana so ne a zakulo wadanda za su rike mukaman jam’iyyar ta APC mai mulki a mazabu, kananan hukumomi da kuma matakan jihohi.

Wani daga cikin kusoshin jam’iyyar, ya shaida wa jaridar cewa su na cikin wani irin mawuyacin hali, ya ce ba su da gamsashen alkaluman ‘yan jam’iyya.

APC NEC

Manyan APC a taro Hoto: www.guardian.ng

“Abin da mu ke da shi a hedikwata, tsurar sunayen ‘yan jam’iyya ne wanda mu ke tunanin cewa an yi ha’inci a rajistar."

Muna da adadin ‘yan jam’iyya, amma sunaye da hotunansu, ya na hannun jihohi. Dole a tattara su, mu iya hada rajista.”

“Ya za a ce Kano ta na da ‘yan APC miliyan hudu, sai kuma mutum miliyan biyu a Legas? Menene adadin mutanen jihar?

“Mutum nawa suka yi rajista a zaben da ya wuce? Ka da mu yaudari kanmu. Akwai matsala!”

Jam’iyyar APC za ta gamu da matsala wajen zabukan muddin ba a tantance rajistocin da ke dauke da cikakken bayanin ‘ya ‘yan jam’iyya da aka yi wa rajista ba.

Rahotun Legit

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN