An kama rikakken dan bindiga a Sokoto bayan ya shigo gari domin sayen maganin kara karfin maza wajen jima'i


Rundunar tsaro ta NSCDC a jihar Sokoto ta kama wani rikakken dan bindiga mai suna Bello Galadima dan shekara 40 a Duniya.

Kakakin hukumar NSCDC na jihar Sokoto Hamza Illela, ya sanar wa manema labarai a Sokoto ranar Talata 27 ga watan Yuli. Ya ce an kama dan bindigan ne a Unguwar Aliyu Jodi da ke Birnin Sokoto lokacin da ya je domin ya saye maganin kara karfin maza wajen jima'i.

Ya ce rundunar ta yi nassarar kama dan bindigan ne da hadin gwiwar jami'anta na sashen ayyukan sirri sakamakon samun bayanan sirri daga al'umma.

أحدث أقدم