An kama matar da ke sayarwa Yan bindigan dajin Kaduna makamai, duba kudi da aka kamata da su


Rundunar yansandan jihar Katsina ta kama wata mata mai suna Aisha Nura a karamar hukumar Batsari bisa zargin safarar makamai, kuma an same ta da makuddan kudi har Naira miliyan biyu da dubu dari hudu N2.4.

Kakakin rundunar yansandan jihar Katsina SP Gambo Isah ya sanar wa manema labarai  ranar Juma'a 30 ga watan Yuli.

Ya ce wadda aka kama Yar asalin garin Baranda ce kuma mai shekara 27 matar wani rikakken dan bindiga ne mai suna Nura Alhaji Mumai.

Ya ce yansanda sun kama ta ne cikin yanayi na zargi da alamar rashin gaskiya bayan ta dauki shattan babur daga Batsari zuwa kauyen Nahuta ranar 25 ga watan Yuli, 2021.

Bayan yansanda sun caje ta ne suka gano tsabar kudi N2,405,000:00K ta boye a kayanta. Wanda ake zargin kudin da take sayar wa Yan bindiga makamai ne a gandun dajin jihar Kaduna.

Sai dai Aisha ta gaya wa yansanda cewa kudin na wani Dan bindiga ne mai suna Nura Alhaji, wanda ke sansanin jagoran Yan bindiga mai suna Abu Radda kuma ya aike ta ne ta karbo masa kudin daga wajen takwarorinsa a gandun dajin jihar Kaduna.


Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE