Ƴan bindiga sun riƙe ɗan saƙo kan zargin samun giɓi na kudin fansa


Shafin BBC Hausa ya ruwaito cewa Ƴan bindigar da suka sace daliban makarantar Islamiyyar nan ta garin Tegina da ke jihar Neja, sun tsare wani dattijo, daya daga cikin mutane shida da suka kai kudin fansar daliban Naira miliyan talatin, bisa zargin cewa kudin ba su cika ba.

Shugaban makarantar Mallam Abubakar Alhassan ya shaida wa BBC Hausa cewa tun farko mutanen ne suka bukaci su biya Naira miliyan 30 kafin sakin ɗaliban da aka kama.

'Mun yi kokari mun sayar da abubuwan da za mu iya siyarwa, kadarori ne da dama, har wani yanki na filin makarantar nan muka siyar muka hada kudin nan, muka tura kwamitin iyayen dalibai da wani dattijo domin su je su basu kudin''

Ya kara da cewa bayan basu kudin ne sai suka bukaci dattijon ya tafi da su domin su kirga kudin da aka basu don tabbatar da cewa sun cika, to da aka tafi ne kuma sai suka kira waya suka ce kudin basu cika ba, babu fiye da Naira miliyan 4, don haka za su rike dattijon a wajensu''

Ya ce a halin da ake ciki iyayen daliban sun yanke shawarar kawai za su zubawa sarautar Allah ido, sun hakura da 'ya'yan nasu har zuwa lokacin da Allah zai kubutar da su, saboda babu wani abu da suke da shi da za su sake basu kuma yanzu.

Jihar Neja

Hukumomin makarantar sun musanta cewa kudin basu cika Naira miliyan 30 ba, inda shugaban makarantar ya ce da hannunsa ya kira kudin, kuma ya tabbatar da cewa sun cika cif cif.

Kwanakin baya ne dai aka samu rahotannin cewa an saki dalibai 11 cikin kusan 150 din da 'yan bingidar suka sace a wannan makaranta ta Salihu Tanko Islamiyya da ke Tegina.

Tuni dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba jami'an tsaro umarnin gaggauta ceto ɗaliban Islmiyyar da aka sace a jihar Neja

Satar dalibai daga makarantnsu a jihohin Najeriya musamman na arewa maso yammacin ƙasar dai ya zama ruwan dare a baya bayan nan. inda masu garkuwar ke neman a biya su makudan kudi kafin sakin yaran da suka sace.

Yanzu satar daliban makaranta a Najeriya ya zama ruwan dare, kuma yanzu satar ɗaliban ta koma har ɗaliban makarantun gaba da sakandare.

A makon da ya gabata ne aka saki ɗaliban Jami'ar Greenfield a jihar Kaduna bayan kashe wasu daga cikinsu. Wannan na zuwa bayan sako ɗaliban Kwalejin gandun daji da ke Kaduna

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN