"Yi abin da na ce kada ka yi abin da na yi" kalma ce ta narko, Imam Muhktar ya tsaga gaskiya kan lamarin


Limamin babban Masallacin Juma'a na jihar Kebbi Imam Muhktar Abdullahi (Walin Gwandu) ya bukaci al'umma Musulmi su guji amfani da kalmar " Ka yi abin da na ce amma kada ka yi abin da na yi". Imam ya gabatar da wannan bukatar ne a cikin hudubarsa kafin Sallar Juma'a a garin Birnin kebbi.

Imam ya ce " Jama'a Musulmi, akwai wata kalma da mutane ke amfani da ita, suna ganin Kamar wani kokari ne ko kyautatawa. Kalmar ita ce KA YI ABIN DA NA CE KADA KA YI ABIN DA NA YI. Wannan kalma ta fito ne daga Turawa."

Imam ya ce hanyar tarbiyyarmu da manufar Turawa ba daya ba ce. Ya kuma yi bayani cewa kalma ce ta barna, ya kara da cewa kalma ce ta narko, wacce ke hana mutum tsayuwa ya yi abin kirki.

Ya.lissafta illolin aiki da wannan kalma tare da gabatar da hujjoji bisa madogara ta Addinin Musulunci, daga karshe ya bukaci al'umma su farga kuma su fahimci sharri da illolin da ke tattare da amfani da wannan kalma.

Daukar nauyi:

Rt. Hon. Hassan Muhammad Shallah (Kwamishinan kananan hukumomi jihar Kebbi)
Alhaji Ibrahim Bagudu (Sarkin Samarin Masarautar Gwandu)

Allah ya saka maku da mafificin alkhairinsa.

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN