Gwamnoni da ministoci a halin yanzu sun isa fadar mai martaba Sarkin Kano don tsara tsare-tsaren bikin auren Yusuf Buhari, dan shugaban kasa, Daily Trust ta ruwaito.
A yanzu haka Yusuf na shirin auren diyar Sarkin Bichi kuma tawagar da ke karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Badaru na jihar Jigawa suna Kano don tsara tsare-tsaren bikin auren.
Sarkin na Bichi kane ne ga Sarkin Kano, wanda a yanzu haka shi ke karbar bakuncin wakilai daga fadar shugaban kasa. Rahoto ya bayyana cewa, iyalai da kusa da nesa sun taru don tsara bikin wanda ake sa ran zai gudana tsakanin watan Agusta da Satumban bana. Karin bayani nan kusa...
Source: Legit
Reported by ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari