Yan bindigan daji na ci gaba da cin karensu ba babbaka a Masarautar Zuru, sun farmaki kauyuka sun sace shanu fiye da 200


Yan bindigan daji kuma barayin shanu suna ci gaba da cin Karen su ba babbaka a Masarautar Zuru da ke kudancin jihar Kebbi. Yan bindigan sun farmaki wasu kauyuka suka sace shanaye kimanin guda 200 ranar Litinin 14 ga watan Yuni. 

Rahotanni sun ce Yan bindigan sun farmaki kauyukan Biki, Sha da wanka, Gora, Duhu, Ikara, Uzugu, Raba kwana, Karomo, Unguwar Bature da sauransu. Maharan sun kora shanayen bayin Allah a wadannan kauyuka.

Sai dai wata majiyar tsaro a jihar Kebbi ta ce maharan sun farmaki al'umman kauyukan ne tun da sanyin safiyar ranar Litinin, suka kora kimanin shanaye 200 na jama'a. Kuma soji da ke Bena sun doshi Yan bindigan amma suka gudu suka ki yin artabu da sojin 

Majiyar ta ce Yan bindigan na tsakanin Diri da Sakaba. Kazalika rahotanni sun ce Yan bindigan sun harbi wani tsoho da bindiga amma bai mutu ba.

Kazalika mun samo cewa Yan bindigan sun dauke wasu mutane, amma daga bisani suka sako su. 

Sai dai wata majiya ta ce ana fargaban Yan bindigan sun kashe mutum daya a kauyen Rambo, Biki da Raba kwana duk an kashe mutum daya a kowanne.

Wannan yana faruwa kasa da mako daya bayan Yan bindigan daji sun kashe kimanin mutum 88 a kauyukan yankin karamar hukumar Danko-Wasagu kuma suka kora shanu masu kimanin 500.

Wata majiyar 
Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN