Yan Bindiga Sun Ƙi Sakin Wani Basarake, Sun Saki Matansa Biyu Duk da An Basu Maƙudan Kuɗi


Yan bindiga sun saki matan Madakin Zungeru, ƙaramar hukumar Wushishi, jihar Neja, bayan an biya kuɗin fansa miliyan N5m, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

A kwanakin baya ne, yan bindiga suka kutsa har cikin gidan basaraken, Mustapha Madaki, suka yi awon gaba da shi da kuma matan shi guda biyu.

An biya maƙudan ƙuɗi a matsayin fansa amma sun ƙi sakin Basaraken

Wata majiya daga ƙaramar hukumar ta bayyana cewa bayan ɗaukan wasu kwanaki ana tattaunawa da yan bindigan. Mutanen garin sun haɗa miliyan N5m daga cikin miliyan N10m da yan bindigan suka nemi a basu da farko.

Bayan tsabar kuɗi miliyan N10m, yan bindigan sun buƙaci a basu manyan wayoyin android guda 100, da mashin Bajaj guda 5, kuma akai su wani wuri da suka faɗa a yankin Madaka, karamar hukumar Rafi.

Majiyar tace: "Da farko yan bindigan sun buƙaci a basu kuɗi naira miliyan N10m, wayoyin hannu 100 da kuma mashin bajaj guda 5, amma a halin yanzun bamu haɗa waɗannan kuɗi ba."

Legit.ng hausa ta gano cewa masu garkuwan sun buƙaci a ƙara musu kuɗi kafin su saki basaraken.

Wani rahoto ya bayyana cewa an kai mata 2 da aka sako wani asibiti a Abuja domin kula da lafiyarsu.

A wani labarin kuma Babban Dalilin da Yasa Ba Zamu Taɓa Rabuwa da Almajiranci a Arewa Ba, Ganduje

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano , yace gwamnonin arewa ba dagaske suke ba wajen ɗaukar mataki a kan kwararar almajirai a jihohinsu, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Gwamnan yace ya zama wajibi gwamnonin jihohi su haɗa kan su sun ɗauki matakin daƙile matsalar.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN