Kungiyar manoma Albasa da kasuwancinta a Najeriya (OPMAN) ta ce za ta katse samar da kayayyaki ga dukkan yankunan kudancin Najeriya daga ranar Litinin matukar gwamnatoci ba su amsa bukatun kungiyar ba.
Daily Trust ta tattaro cewa daya daga cikin bukatun OPMAN shi ne cewa membobin kungiyar da suka yi asara sakamakon rikicin kabilanci da addini a Kudancin dole ne a biya su yadda ya kamata.
Sauran sun hada da maido da doka da oda a wadannan yankuna tare da yin cikakken bincike don gano musabbabin wadannan hare-hare kan mambobinsu.
PMAN ta kuma yi kira ga al'ummomin da su mutunta 'yancin da kundin tsarin mulki ya ba 'yan kasuwar arewa a jihohinsu.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron kungiyar a Sakkwato a karshen mako, Shugaban OPMAN, Aliyu Isa, ya lura cewa mambobin kungiyar sun yi asarar albasa da kadarorin da suka kai kimanin Naira biliyan 4 da rabi a hare-hare daban-daban a kudu.
A cewarsa, a lokacin rikicin Aba a jihar Abia, kungiyar ta rasa mambobinta uku, yayin da kimanin tirela 30, motoci 9, shaguna 50 da buhunan albasa 10,000, da sauran abubuwa masu muhimmanci na mambobinsu.
A garin Shasa na jihar Oyo, ya ce an yi asarar rayuka 27, tirela biyar, buhun albasa 5,600, motoci 12 da sauran abubuwa masu daraja.
Isah ya kara da cewa an wa mambobin fashin albasa mai darajar Naira miliyan 13 a jihar Imo.
A baya kungiyar ta yi gargadin cewa, za ta tsunduma yajin kai kaya kudu matukar ba a saurari damuwarsu ba, in ji BBC.
Source: Legit Nigeria
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari