Hotunan yadda Shugaba Buhari ya gana da Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu kan Ɗaliban FGC da aka sace


Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya gana da gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi kan ɗaliban makarantar sakandiren gwamnatin tarayya da aka sace a jihar.


 Shugaban ya gana da gwamnan ne domin jin yadda lamarin ya faru da kuma inda aka kwana akan lamarin. Gwamnan Bagudu ya yiwa Buhari bayanin halin da ake ciki da kuma matakan da aka fara ɗauka domin kuɓutar da ɗaliban Shugabannin biyu sun gana ne da daren jiya Talata a fadar shugaban Ƙasa dake Abuja, kamar yadda Buhari Sallau ya rubuta a shafinsa na facebook. 


A makon da ya gabata ne yan bindigan suka kai hari makarantar FGC Birnin Yauri, inda suka yi awon gaba da wani adadi na ɗalibai da malamai guda huɗu. Legit.ng hausa ta tattaro muku wasu daga cikin ra'ayoyin mutane kan wannan ganawar da aka yi. Abdulganiyu Jimoh, yace: "Wannan yazo lokacin da ya dace domin yanzun jami'an tsaron mu na ɗaukar matakin da ya dace da yan ta'addan." 


Usman Mu'azu Ksauri, yace: "Masha Allah, Allah yasa a tattauna alkairi." A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Saki Hotunan Halin da Malamai, Ɗaliban Kebbi Ke Ciki Yan bindigan da suka yi awon gaba da ɗalibai a FGC Birnin Yauri sun saki hotunan waɗanda suka kama. A makon da ya gabata ne maharan suka dira makarantar sakandiren, inda suka yi awon gaba da wani adadi na ɗalibai. 

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN