Yan ta'adda sun kashe yansanda 2 NSCDC 2 da farar hula 2 a harin kampanin yan China a Zamfara


Yan ta'adda sun kashe yansanda Mopol 2 jami'an NSCDC 2 da farar hula 2 lokacin wani harin bazata da suka kai kampanin PGP a kauyen Gora da ke Birnin Tudu a karamar hukumar Bakura a jihar Zamfara ranar Litinin 14 ga watan Yuni. HumAngle ta ruwaito.

Yan ta'addan sun farmaki kampanin PGP mallakin Yan kasar China wanda suke gudanar da aikinsu a Madatsan ruwa na Bakalori da ke karamar hukumar Maradun. Ganau ba jiyau ba ya gaya wa HumAngle cewa Yan ta'addan sun farmaki kampanin ne lokacin da jami'an tsaron suke cikin Sallar Magariba. 

Kazalika Yan ta'addan sun banka wa mota kirar Hilux na jami'an tsaron wuta, suka kwashe bindigoginsu, daga bisani suka tafi.

An kashe wani Sajen na yansanda mai suna Zaharaddeen Sani, wanda ke aiki a ofishin yansanda na Talata Mafara, da wani farar hula mai suna Tanimun Muhammed, wanda dan garin Talata Mafara ne. Sai dai ba a sace kowa ba a lokacin farmakin.

Jami'an tsaron da aka kashe a farmakin sun hada da Ahmed Murtala, CTU Sgt Yusuf Usama, Sgt. Ibrahim Bello, Sgt. Zaharadden Yusuf, NSCDC Sani Abubakar da Direba  Tanimu Muhammad.

An raunata jami'in NSCDC Sirajo Aliyu, kuma yana samun kulawan Likitoci a Federal Medical Centre (FMC) Gusau.

Sai dai har yanzu Shelkwatar yansandan jihar Zamfara bata fitar da bayani kan lamarin ba kawo yanzu.

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN