Type Here to Get Search Results !

Sojoji sun kama matasa 73 tare da babura 47 a hanyarsu ta zuwa jihar Imo daga Nasarawa


Sojoji na Runduna ta Musamman ta Birged 72, Sojojin Najeriya, da ke Makurdi a daren Litinin, 14 ga Yuni sun kama matasa 73 daga jihar Nasarawa a kan hanyarsu ta zuwa Imo.

A cewar wani rahoto da jaridar Nigerian Tribune ta fitar, ta ce sojojin da ke aiki a kan rahoton tsaro ne suka cafke matasan majiya karfi wadanda aka loda a manyan motoci biyar.

Haka kuma an ga babura kirar Bajaj guda 47 tare da matasan. An ce motocin na daukar wasu ma'adanai daga jihar Filato zuwa wani kamfani da ke Fatakwal.

Gwamnatin Benue ta nuna damuwa, ta yabawa sojoji

Mataimakin gwamnan jihar Benuwe, Benson Abounu, wanda ya ziyarci barikin a ranar Talata, 15 ga watan Yuni ya yaba wa sojoji kan kamun.

Ya nuna farin ciki cewa duk da kokarin gujewa kamun, sojoji sun sami nasarar cafke manyan motocin tare da kama mutanen.

Ya nuna mamakinsa kan yadda za a samu irin wadannan dimbin samarin daga jiha daya a tare zuwa jihar Imo mai fama da rikici.

Sojojin Najeriya sun bayyana yadda aka kamasu

Kwamandan runduna ta musamman ta Birgede 72, Laftanar Kanar AD Alhassan ya ce mutanen nasa sun yi aiki ne bisa rahoton tsaro.

Ya bayyana cewa suna samun rahoton cewa wasu manyan motoci na hanyar tafiya zuwa Makurdi sai suka yunkura don tare motocin nan take.

Kungiyar Arewa Ta Gargadi 'Yan Arewa Kan Zuwa Yankin Kudanci

A wani labari na daban, kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) ta gargadi ‘yan Arewa kan tafiya zuwa yankin Kudu maso Gabas a yanzu saboda halin da ake ciki na rashin tsaro.

Ta ba da shawarar cewa idan tafiyar ta zama dole, to a yi amfani da jami'an tsaro a ciki, Nigeria Tribune ta ruwaito.

Wannan ya na kunshe ne cikin wata sanarwa da Shugaban ACF na kasa, Cif Audu Ogbe, ya fitar a ranar Litinin.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies