Sanatoci Zasu Fallasa Sunayen MDAs da Suka Ɓatar da Ƙudin Gwamnati, duba cikakken bayani


A ranar Talata, Sanatoci sun sha alwashin zasu fara bayyana sunayen ma'aijatu, sashi-sashi da hukumomi (MDAs) na gwamnatin tarayya waɗanda suka kasa kare tuhumar da ofishin Adita Janar na ƙasa (AuGF) ya musu, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Shugaban sanatoci, Sanata Ahmad Lawan, shine ya nuna haka bayan an gabatar da rahoton kwamitin kula da asusun fili.

Kwamitin ya gabatar da rahotonsa ne a kan binciken da ya gudanar bayan ofishin AuGF ya fitar da rahoto a shekarar 2015.

Shugaban kwamitin, Sanata Matthew Urhoghide, a yayin gabatar da rahoton yace wasu daga cikin MDAs sun gaza kare kansu akan zargin da ofishin AuGF ya musu.

Sanata Urhoghide, Yace: "Da yawan ma'aikatun gwamnatin tarayya da hukumoni sun ƙi zuwa su kare kansu kan tuhumar ɓatar wasu kuɗaɗe da ofishin AuGF ya fitar a rahotonsa."

A wani labarin kuma Wani Fitaccen Malami Yace Haramun Ne Yin Amfani da Alamar Dariya a Facebook

Wani fitaccen malamin addinin musulunci yace haramun ne amfani da alamar dariya a facebook domin muzgunawa wani, kamar yadda BBC hausa ta ruwaito.

Malamin mai amfani da suna ɗaya, Ahmadullah, yana da tarin mabiya a kafafen sada zumunta.

Source: Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN