Najeriya Zata Samar Da Manyan Wayoyin Hannu Ga Ƙasashen Africa, Pantami


Ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Dr. Isa Pantami yace Najeriya tana da damar da zata samar da layukan waya da manyan wayoyin hannu ga ƙasashen Africa, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Ministan ya faɗi haka ne a wani taro da jam'iyyar APC ta shirya ranar Alhamis a Sakateriyar jam'iyyar dake Abuja.

APC ta shirya taron ne ga hadiman gwamnati su baje kolin nasarorin da suka samu tun sanda suka shiga ofis ga yan Najeriya.

Yayin da Pantami ke jawabi a wajen taron, ya tabbatar da cewa daga yanzun za'a daina shigo da layukan waya daga ƙasashen waje da sauran kayan sadarwa saboda kashi 60-70% Najeriya zata rinƙa samar da su.

A cewar ministan Najeriya tana da ƙarfin da zata iya samar da layukan waya 200 miliyan duk shekara.

Pantami yace: "Munzo da sabon tsari wanda nan da shekara 2 zuwa 3, mafi karanci kashi 60-70% na abinda muke buƙata ta ɓangaren sadarwa zamu samar dashi a cikin gida Najeriya."

"Lokacin da wannan gwamnatin tazo, layukan waya bama iya yi sai an kawo mana daga waje. Amma yanzun gwamnatin tarayya ta baiwa masu zaman kansu damar su samar da layukan waya, ba wai ga ƙasa kaɗai ba harda kasashen Africa."

"Muna da ƙarfin da zamu iya samar da layukan waya 200 miliyan a shekara. Yanzu a Najeriya muna samar da manyan wayoyin hannu."

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN