Mutumin da Ya Fi Kowa Iyalai a Duniya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya


Wani mutum a arewa maso gabashin Indiya, wanda ya fi kowa yawan iyali a duniya, ya mutu.

Ziona Chana mai shekaru 76. Iyalinsa sun ce ya yi fama da ciwon suga da hawan jini wanda ya yi sandiyyar mutuwarsa, BBC ta ruwaito.

Mista Chana yana da mata 39 da yara 94 da kuma jikoki da yawa.

Ya zauna tare da dukkanin iyalinsa a wani gidan bene hawa hudu da ke wani kauye mai tsaunuka a jihar Mizoram, da ke iyaka da kasar Myanmar a yankin Asiya.

Jami'ai sun ce gidan ya zama wani babban wurin jan hankali ga 'yan yawon bude ido saboda yawan iyalin mutumin.

Mista Chana ya shugabancin wata kungiyar mabiya addinin Kirista da ke da'awar ba da damar auren mata fiye da daya. Ya fara yin aure yana da shekara 17.

Babban Ministan Mizoram Zoramthanga ya yi wa iyalansa ta’aziyya kuma ya ce dangin su ne babban wurin jan hankalin ‘yan yawon bude ido a jihar, India Tv News ta ruwaito.

A wani labarin, Elisane Silva, duk da cewa ba a hukumance ba, amma itace mace mafi tsayi a kasar Brazil, in ji rahoton Daily Mail.

Budurwar da ta fito daga Salinopilis a kasar Brazil ta fara lura da saurin girmanta lokacin tana da shekaru 10.

A baya tsawonta yakai kafa 5 da inci 9 to amma a yanzu ta kai kafa 6 da inci 8.

Budurwar mai shekaru 26 ta ce ta sha wahala ta fuskar zagi da izgili saboda tsayinta kuma sau da yawa takan kulle kanta domin ta nisanci jama'a, Metro.co.uk ta ruwaito.

Source: Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN