Matawalle ya ba Zamfarawa wa'adin kwana 7 su mika makaman da suka mallaka


Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya umarci dukkan mazauna jihar da su mika makaman da suka mallaka ba bisa ka'ida ba ga hukumar 'yan sanda mafi kusa dasu a cikin kwanaki bakwai kacal.

Gwamnan ya bada wannan umarnin ne yayin saka hannu a wata takardar shela ga dukkan jihar Zamfara, kamar yadda hadiminsa a harkar yada labarai, Zailani Bappa ya sanar a ranar Laraba.

Kamar yadda takardar ta nuna, umarnin ya biyo bayan umarnin da shugaban kasa ya bada na harbe duk wanda aka kama da makamai ba bisa ka'ida ba a take, Daily Nigerian ta ruwaito.

Takardar ta ce: "Domin tabbatar da karfin ikon da nake da shi, ni Dakta Bello Mohammed, ina bada wadannan umarnin.

"Dukkan makamai dake hannun jama'ar jihar Zamfara ba bisa ka'ida ba, a mika su ga ofishin 'yan sanda mafi kusa a cikin kwanaki bakwai daga ganin wannan sanarwan," takardar ta sanar da hakan.

Bappa ya kara da cewa, gwamnan yayi kira ga mazauna jihar da su kasance masu kiyaye doka domin samun damar shawo kan matsalar tsaro a jihar.

A wani labari na daban, gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya sallami dukkan kwamishinoninsa da masu mukaman siyasa na jihar.

Kamar yadda takardar da mai bashi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Zailani Bappa ya fitar a ranar Litinin ta nuna, gwamnan ya bukaci dukkan kwamishinoni da masu mukaman siyasa na jihar da su koma gida su huta.

Kamar yadda wasikar da Zailani Bappa ya wallafa a shafinsa na Facebook ta bayyana, gwamnan yace wannan sallamar bata shafi duk wata hukumar da kundun tsarin mulkin kasar Najeriya ya kafa ba a jihar.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN