Malami ya yi umarnin hukunta wadanda suka ki daina amfani da Twitter


Ministan Shari'a na Najeriya Abubakar Malami ya yi umarnin a yi gaggawar hukunta duk mutumin da ya ki bin umarnin gwamnatin kasar na daina amfani da shafin Twitter.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ministan Umar Jibrin Gwandu ya aike wa manema labarai ranar Asabar, ya ambato Malami yana umartar daraktan gabatar da kara na tarraya ya yi hanzarin tuhumar mutanen da suka ki bin umarnin gwamnati.

Ya umarce shi da ya hada gwiwa da Ma'aikatar Sadarwa da Tattalin arzikin intanet ta kasar da hukumar da ke sanya ido kan kamfanonin sadarwa da sauran hukumomin da ke da alaka da irin wannan aiki domin ganin hakan ya tabbata.

A ranar Juma'a ne gwamnatin kasar ta dakatar da amfani da Twitter a Najeriya kwanaki kadan bayan shafin ya goge wani sako da shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa inda yake gargadin masu tayar da rikici a kudu maso gabashin kasar.

Rahotun BBC

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN