Madalla labari mai dadi: An gabatarwa Buhari da wayar hannu na farko da aka yi a Najeriya


A ranar Laraba, 9 ga watan Yuni, Otunba Niyi Adebayo ya gabatarwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da wayar hannu na farko da aka yi a Najeriya.

An gabatar da wayar ne a yayin taron Majalisar zartarwa ta Tarayya (FEC) wanda aka gudanar a Fadar Shugaban Kasa, Abuja.

Bugu da ƙari, a taron, shugaban kasar ya rantsar da kwamishinonin tarayya na Hukumar Kula da Yawan Jama'a (NPC) da Hukumar Kula da ma’aikatan Tarayya (FCSC).

Hadimin shugaban kasar a kafofin watsa labarai na zamani, Buhari Sallau ne ya bayyana hakan a cikin wani wallafa da yayi a shafinsa na Facebook.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama’a kan wallafar:

Umar Haruna Fada ya ce:

“Wannan abin birgewa ne, muna son irin wannan rashin nasara na rantse .... Allah ya albarkaci PMB.”

Lawal Abubakar ya yi martani:

Aiki mai kyau ya Shugaban kasa.”

Aliyu Sulaiman Idris ya ce

:“Mun yi imanin Najeriya za ta yi nasara insha Allah.”

A wani labarin, babban Bankin Duniya ya sake nazarin bunkasar tattalin arzikin da Najeriya ta yi hasashe, wanda ya kara kimanta yawan kayan cikin gida na 2021 zuwa 1.8%.

Cibiyar Bretton Wood ta daga ci gaban tattalin arzikin Najeriya daga 1.1% zuwa 1.8% na wannan shekarar, yayin da ta bayyana cewa GDP zai kara karuwa zuwa 2.1% a shekara mai zuwa, da kuma 2.4% a shekarar 2023 ta badi.

Tattalin arzikin Afirka kuwa an sake daga shi zuwa sama har 2.8% a shekarar 2021, kuma a shekara mai zuwa, tattalin arzikin yankin ana hasashen zai kai 3.3%. An kiyasta tattalin arzikin duniya cewa zai tashi da kashi 5.6%.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN