Type Here to Get Search Results !

Kungiyar ESN Ta Kashe Bokanta Bisa Yin Tsafin da Bai Yi Tasiri Kan ’Yan Sanda Ba


Mambobin haramtacciyar kungiyar tsaro ta Gabas (ESN) sun harbe wani mutum, mai suna Paschal Okeke, wanda ke kera “layar cin nasara” ga kungiyar saboda gazawar layarsa wajen karesu na tsawon shekaru, in ji ‘yan sanda a jihar Imo. 

Wata sanarwa daga ‘yan sanda ta ce, kungiyar ta fusata da cewa layar, wanda ya kamata ta sa ba za a iya cin nasara a kansu ba kuma su tsere wa farmakin jami’an tsaro ba ta yi wani tasiri ba. 

‘Yan sanda sun ce kisan ya biyo bayan samun nasarar 'yan sanda na kai samame a maboyar kungiyar da kuma ragargazar mambobin haramtacciyar kungiyar IPOB, Daily Trust ta ruwaito.

 'Yan sanda sun ce kisan ya faru ne a ranar 25 ga Yuni, kuma bayan harbe shi, sun kone gawarsa kurmus, hakazalika sun cinna wa gidansa wuta. An fara amfani da tsafi a kudu maso gabas don magance matsalar tsaro Wani rahoton da Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa an ajiye wani kambun tsafi a gaban babban ofishin 'yan sanda na jihar Abia da nufin kare hare-haren 'yan bindiga. 

An gano cewa mazauna Bende road a Umuahia, babban birnin jihar, a ranar Talata 22 ga watan Yuni sun farka sun ga an ajiye kambun tsafin a inda aka takaita zirga-zirgan mutane da ababen hawa. Duk da cewa a yanzu Legit.ng bata samu damar tabbatar da lamarin ba, rahoton da jaridar ta wallafa ya ambaci cewa mazauna unguwar sunyi ikirarin cewa an ajiye kambun tsafin ne don kare jami'an tsaro daga 'yan bindiga. 

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies