Kimanin Yan bindigan daji 500 da goyo kan babura sun farmaki kauyukan Danko-Wasagu, sun kashe mutane da yawa


Rahotanni daga karamar hukumar Danko-Wasagu da ke Masarautar Zuru a kudancin jihar Kebbi sun yi zargin cewa mutane da dama sun mutu bayan wani mumunan farmakin Yan bindigan daji kan wasu kauyuka ranar Alhamis.

Rahotanni sun yi zargin cewa, kimanin Yan bindigan daji su 500 ne goye da jama'arsu kan babura suka farmaki kauyen Yabuga da sauran kauyuka da ke wannan kewaye.

Yanzu haka ana cikin jimami da zaman makoki a garuruwa da kewaye da lamarin ya shafa, bayan an kawo gawakin mutane da suka kai dauki lokacin farmakin na Yan bindigan a kauyen Yabuga.

A mazabar Kanya, ana zargin ana kan tattara sunaye da adadin gawakin mutane da suka je kai dauki daga kauyukan Chediya, Dgoga, Mashekari, Zuttu, Dpindu, Kimpi, Koro, Gwazawa da sauransu, amma suka rasa ransu.

A garin Kanya, tuni aka haka kabarbura tare da yi wa wadanda suka mutu sutura.

Mahukunta kan harkar tsaro a jihar Kebbi na cikin yanayin ko ta kwana kan lamarin. Tuni wasu ke yi wa farmakin Yan bindigan kan kauyukan kallon shikamakin tabbacin tabarbarewan tsaro a Masarautar Zuru da ke kudancin jihar Kebbi.

Kawo yanzu wata majiya mai tushe kan sha'anin tsaro a jihar Kebbi ta tabbatar cewa yanzu haka masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a fadin jihar Kebbi suna tattara bayanai kan hakikanin abin da ya faru lokacin farmakin da Yan bindigan daji suka kai kauyukan karamar hukumar Danko-Wasagu.

Kokarinmu na jin ta bakin jami'in hulda da jama'a na rundunar yansandan jihar Kebbi kan lamarin ya ci tura sakamakon sha'anin aiki.

Ku biyo mu domin cikakken labari......


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN