Kebbi: Sojoji sun sake ragargaza Yan Bindiga sun kuɓutar da Malami da wasu Dalibai da aka sace a Birnin Yauri


Rundunar sojin ƙasa ta bayyana cewa jami'anta sun sake kutsawa cikin daji domin kuɓutar da ɗaliban da aka sace a Birnin Yauri, kuma sun samu nasarar sake kuɓutar da wani malami da ɗalibai 3, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

A yayin wannan operation, Sojoji sun kashe ɗan ta'adda ɗaya tare da kwato mashina 9, waɗanda suke mallakin ɓarayin.

Kakakin rundunar soji, Brig. Janar Onyema Nwachukwu, shine ya bayyana haka, yace an ƙara tura wasu jami'an soji domin tsaftace yankin da kuma hana ɓarayin tserewa.

Yace: "Malami ɗaya da wasu ɗalibai uƙu sun kuɓuta a wani Operation da sojoji suka fita ranar Asabar a Makuku."

"Sojoji sun kashe mutum ɗaya daga cikin ɓarayin, sannan sun kwato mashina 9 da kuma wayoyin hannu guda huɗu."

"Rundunar soji ta ƙara tura jami'ai yankin domin su mamaye dajin kuma su hana ɓarayin tserewa."

A baya sojoji sun kuɓutar da ɗalibai 5

Tun a ranar jumu'a da ta gabata, gwarazan jami'an soji suka yi artabu da ɓarayin, inda suka kuɓutarda malamai biyu da ɗalibai 5.

Nwachukwu yace: "Idan zaku iya tunawa, a ranar Jumu'a 18 ga watan Yuni, sojoji sun samu nasarar kuɓutar da malamai 2 da ɗalibai 5 daga hannun yan bindigan."

A wani labarin kuma El-Rufa'i Ya Yi Kakkausan Gargaɗi Ga Mutanen Dake Toshe Hanyar Kaduna-Abuja

Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i ya gargaɗi mutanen jihar sa a kan toshe hanyar Kaduna-Abuja, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Gwamnan yayi wannan gargaɗi ne yayin ziyarar ta'aziyya da yakai yankunan, inda ya tattauna da mutanen yankunan.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN