Hotunan Yarinyar da Ta Fi Kowa Tsawo a Brazil Tare da Mijinta


Elisane Silva, duk da cewa ba a hukumance ba, amma itace mace mafi tsayi a kasar Brazil, in ji rahoton Daily Mail.

Budurwar da ta fito daga Salinopilis a kasar Brazil ta fara lura da saurin girmanta lokacin tana da shekaru 10.

A baya tsawonta yakai kafa 5 da inci 9 to amma a yanzu ta kai kafa 6 da inci 8.

Budurwar mai shekaru 26 ta ce ta sha wahala ta fuskar zagi da izgili saboda tsayinta kuma sau da yawa takan kulle kanta domin ta nisanci jama'a, Metro.co.uk ta ruwaito.

Yadda ta fara soyayya da wani dan shekaru 31

Elisa daga baya ta yi aurenta tare da wani mutumi mai suna Francinaldo Da Silva Carvalho a cikin shekarar 2015.

A cewarta, sun hadu ne a shekarar 2011 kuma sun fada tsananin soyayya da kaunar juna. Gamayyar ta yi kyau, domin kuwa sun samu karuwar da.

Elisa ta yaba da gaskiyar cewa mijinta na son ta duk da bambancin tsawonsu kuma bai taba ganin hakan a matsayin matsala ba.

Ta ce:"

Na ji wata alaka nan take a lokacin da na hadu da shi, kuma ban ma lura da tsayinsa ba.

 "Tsawon Francinaldo bai wuce kafa 5 da inci 4, wanda na dara shi da kafa kusan biyu - amma ban damu ba.

 "Duk da cewa yana sane da tsayina da yanayina, bai yi wata munanan maganganu ba, kuma bai taba nuna damuwa ba."

A wani labarin, Wata sanarwa da wata mai magana da yawun gwamnati, Phumla Williams ta yi kwanan nan, ta bayyana cewa gwamnati ba ta da wata shaida da ke nuna cewa wata mata Gauteng mai suna Gosiame Thamara Sithole ta haifi jarirai 10 a lokaci guda.

"Gwamnati ta kasa tantance sahihancin waccar haihuwar a cibiyoyinmu," in ji wani bangare na sanarwar da Williams ta fitar.

Tun da farko an samu shakku game da labarin haihuwar mai ban mamaki na wata matar da aka ce ta haifi jarirai 10 a kasar Afrika ta Kudu.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN