Hotunan cikin katafaren gidajen mai kampanin Facebook Mark Zuckerberg masu darajar N131b


Mamallakin Facebook, Mark Zuckerberg yana daya daga cikin jama'a masu son tara kadarori.

Duk da 'ya'yansa biyu kacal masu shekaru 3 da 5, biloniyan yana da jerin katafaren gidaje da kadarori masu yawa da ya siya da sunansa.

Palo Alto, California mai darajar $50 miliyan (N20.5 billion)

Katafaren gidan Palo Alto dake California yana daya daga cikin gidajen da Zuckerberg yake kauna kamar yadda NYpost ta ruwaito.

Wannan kyakyawan gidan an gano cewa dan kasuwan ya siye shi ne shekara daya kafin ya auri matarsa.

Kamar yadda Architectural Digest suka ruwaito, ya siya gidan kan kudi $7 miliyan kuma yana da dakunan bacci 15 da bandakuna sama da 16. Gidan yana da fadin taku 20,000 kuma yana da wurin wanka da sauran ababen more rayuwa.

Lake Tahoe, California mai darajar $59 miliyan (N24.1 biliyan)

Zuckerberg na kaunar California a bayyane saboda gidan da ya mallaka a Lake Tahoe. Gidan hutun an gina shi ne a kusan aka 10 kuma yana da darajar N24.1 biliyan, ya siye shi a 2018.

Gidan mai girman kafa 5,322 yana da dakunan bacci shida, bandakuna biyar, tafki mai fadin kafa 400, dakin baki da garejin mota, Permit records suka tabbatar.

A wani labari na daban, kkungiyar matasan arewa (AYA) ta ce ta shirya fito na fito da duk mai barazana ga shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Abdulrasheed Bawa.

Wannan na zuwa ne bayan kwanaki kadan da yace yana samun barazanar mutuwa saboda manyan da ya addaba a kan rashawa.

Marasa rinjaye a majalisar wakilai a ranar Alhamis sun yi kira ga gwamnatin tarayya da kada su yi watsi da wannan barazanar, Daily Trust ta ruwaito.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN