Gwamnatin Najeriya ta dakatar da shafin Tuwita a Najeriya.


Wata sanar da ma'aikatar yada labarai da al'adu ta fitar, ta ce Minista Lai Mohammed ne ya ba da sanarwar a Abuja a ranar Juma'a.

Sanarwar ta ce Minista Mohammed ya ce ana amfani da shafin wajen raba kawunan ƴan ƙasar.

Lai Mohammed ya kuma ce ya bai wa hukumar kula da gidajen rediyo da talbijin ta ƙasar NBC ta fara shirye-shiryen ba da lasisi ga kafafen yaɗa labarai na intanet.

Sai dai gwamnatin NAjeriyar ba ta fayyace abin da take nufi da wannan mataki ba ya zuwa yanzu.

Wannan mataki na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da shafin Tuwita ya goge wani saƙo cikin jerin saƙwannin da Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa yana gargaɗin ƴan awaren IPOB.

Tun bayan cire saƙon shugaban ƙasar fadar Shugaba Buhari ta ce tana sane da matakin da Twitter ya ɗauka, kuma ta aika da buƙatar neman jin dalilin da ya sa kamfanin ya goge saƙon.

Tuni dai kungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta ce za ta kalubalanci matakin gwamnatin a kotu, a wani sako da ta wallafa a Tuwita din.

Sakon Buhari

ASALIN HOTON,TWITTER

Bayanan hoto,

Wannan shi ne saƙon da Tuwota ya goge na Shugaba Buhari

Me ƴan Najeriya ke cewa?

Jim kaɗan da fitar da wannan sanarwa sai ƴan Najeriya suka fara tofa albarkacin bakinsu a shafukan sada zumunta musamman Tuwitar.

Tuni aka ƙaddamar da maudu'ai har huɗu a shafin na Tuwita don tattaunawa kan batun, da suka haɗa da #So Twitter da aka yi amfani da shi kusan sau miliyan ɗaya a ƙasa da ɗaya da #Twitter in Nigeria 100,000, da #Using Twitter da aka yi amfani da shi sau 239,000.

Sannan akwai maudu'in #Federal Government mai 36,000 da kuma #TwitterBan mai saƙonni 1,384. AKwia kuma irin su #Jack da #Lai Mohammed da #Twitter in Nigeria da #Suspending Twitter da dai sauran su.

Ƴan ƙasar da dama ne suka dinga bayyana ra'ayoyi daban-daban kamar haka:

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar adawa ta PDP a 2019 Alhaji Atiku ya wallafa cewa: "Ina fatan kar wannan ya zama saƙona naƙarshe a Tuwita."

Kauce wa Twitter, 1

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 1

Jibrin Ibrahim tsohon shugaban Cibiyar Binciken Harkokin Dimokraɗiyya CDD shi ma ya rubta: "Ministan Yada Labarai da Al'adu Lai Mohammed, ya dakatar da Tuwita a Najeriya saboda a cewarsa ana amfani da kafar wajen raba kan ƴan ƙasar. To hakan yana nufin idan babu Tuwita ana da tabbacin kan ƴan ƙasar zai haɗu ne?"

Tsohon sanatan yankin Kaduna Ta Arewa Sanata Shehu Sani ma cewa ya yi: "Dakatar da Tuwita, jawowa kai abin faɗa ne."

Arewa Twittér kuwa cewa ya yi: "Ina goyon bayan wannan dakatarwa duk kuwa da cewa ina samun kuɗ a Tuwita, amma wannan ne mataki mai kyau da gwamnatin tarayya ta dauka da ya birge ni."

Rahotun BBC


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN