Gwamnan jihar Kebbi ya yi alkawarin shiga daji domin yaƙi da Yan Bindiga


Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi, yayi alƙawarin shiga cikin mafarauta domin bin sawun yan bindigan jihar, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Da yake jawabi ga mafarauta dake taimakawa wajen yaƙi da rashin tsaro, Gwamna Bagudu wanda yake tare da gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, yace da zaran ya samu rahoton tsaro daga jami'an soji, zai haɗe da maharauta a filin yaƙi.

Gwamnan yace: "Zamu fita yaƙi, kuma kamar yadda na yi alƙawari, duk ranar da zan fita ba za'a ganni a ofis ba. Kuma akwai wasu gwanonin da zasu baro mutanen su, su zo mu shiga filin yaƙi da su."

"Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, tare da jami'an tsaro suna iya bakin kokarin su. Amma duk da haka muna buƙatar mu shirya kan mu, mu sanya kaki, mu tinkari waɗannan yan ta'addan."

"Addinin musulunci da na kiristanci ya bamu damar sadaukar da rayuwar mu wajen kare martabarmu, dukiyoyin mu da imanin mu."

Fayemi ya jajantawa Gwamnati da mutanen Kebbi kan satar ɗaliban FGC

Da yake jawabi ga mafarautan, Fayemi yace yazo jihar ne a bisa wakilcin ƙungiyar gwamnoni ta ƙasa NGF.

Yace: "Mun zo nan ne domin jajantawa ɗan uwanmu, Gwamna Atiku Bagudu da kuma al'ummar jihar Kebbi kan abu mara daɗi da ya faru a makarantar FGC Birnin Yauri."

A wano labarin kuma Har Yanzun Bamu Gano Adadin Ɗaliban da Aka Sace a Kebbi Ba, Rundunar Yan Sanda Ta Yi Cikakken Bayani

Hukumar yan sanda tace har yanzun ba ta gano adadin ɗaliban da yan bindiga suka sace a jihar Kebbi ba, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Kakakin yan sandan jihar, DSP Nafi'u Abubakar, shine ya bayyana haka ranar Jumu'a a Birnin Kebbi.

Source: Legit Newspaper

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN