Gwamnan Arewa Ya Ƙaddamar da Jami'an Tsaro Na Musamman a Jiharsa


A ƙokarinsa na dawo da zaman lafiya a jihar Neja, Gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello, ya kaddamar da sabbin jami'an tsaro na musamman (SVC) da zasu gudanar da aikin su a jihar, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

A cewar gwamnan, sabbin jami'an sa kai da ya ƙadɗamar SVC, za su yaƙi duk wasu yan ta'adda da suka hana jihar Neja zaman lafiya.

Gwamna Bello yace wannan shine karon farko, amma ya ƙara da cewa za'a sake ɗaukar wasu da dama a basu horo, sannan a tura su ƙananan hukumomin jihar.

Hakazalika, gwamnan ya damƙa sabbin motocin operation guda 20, da kuma mashina 20 ga sabbin jami'an domin gudanar da aikinsu.

Rahotanni sun bayyana cewa zuwa yanzun, gwamnatin Neja ta samar da motocin Operation 89, mashin 283, Kekuna 30 da kuma keke nafef 4 ga jami'an tsaron jihar domin inganta tsaro a faɗin ƙananan hukumomi 25 dake faɗin jihar.

Daga cikin tawagar jami'an da suka amfana da irin waɗannan kayan aikin akwai, Karamin Goro, Sharan Daji, Girgizan Daji, Gama Aiki, Ayem Akpatuma I & II, Puff Adder I & II da sauran su.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN