Saudi Arabia: Abin da ya sa kasar ta takaita amfani da amsa-kuwwa wajen kiran Sallah


Hukumomi a Saudiyya sun kare matakin da suka dauka na takaita sautin amsa-kuwwa a masallatai.

Ma'aikatar Harkokin Addini ta sanar a makon jiya cewa za a rage karar dukkan amsa-kuwwar da ke masallatan kasar zuwa kashi daya cikin uku na kararsu.

Ministan Ma'aikatar Abdullatif al-Sheikh ya ce sun dauki matakan ne bayan an kai musu korafe-korafe game da yadda masallatan suke kure amsa-kuwwa, lamarin da ke damun jama'a.

Sai dai matakin ya jawo kakkausan suka a shafukan sada zumunta.

Lamarin ya sa an kirkiri maudu'in da ke kira a haramta amfani da kida da waka masu karfi a wuraren sayar da abinci da shan shayi a kasar.

Al-Sheikh ya ce mutanen da suka yi korafi sun hada da iyayen da ke cewa amsa-kuwwar suna hana 'ya'yansu barci.

Da yake jawabi ta bidiyo da aka nuna a gidan talbijin na kasar, Al-Sheikh ya ce mutanen da ke son yin sallah ba sa bukatar su jira ladan ya kira sallah.

Ya bayyana mutanen da suka soki matakin a shafukan intanet a matsayin "makiyan kasar nan" sannan ya yi zargin cewa "suna so su yaudari 'yan kasa".

An dauki matakin ne yayin da Yarima Mohammed bin Salman mai jiran gadon sarautar kasar yake yunkurin kawar da tsattsauran ra'ayin da ake fama da shi a kasar.

Tuni aka sassauta wasu tsauraran matakai da 'yan kasar suka dade da su, cikinsu har da haraamta wa mata tukin mota.

Sai dai Yariman yana hana fadin albarkacin baki, inda aka kama dubban mutane saboda bayyana ra'ayoyinsu.

Rahotun BBC

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN