Duba abinda tsohon Gwamnan Zamfara Abdulazeez Yari ya ce kan komawar Gwamna Matawalle jam'iyar APC



Tsohon gwamnan Zamfara, AbdulAziz Yari, a ranar Litinin ya yi maraba da magajinsa, gwamna Bello Matawalle, zuwa jam'iyyar All Progressive Congress (APC).


Ana sa ran Matawalle zai sanar da sauya shekarsa daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Talata.

Yari, a ganawar da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar shiyar Zamfara suka yi a Kaduna, ya ce suna lale marhabun da Matawalle zuwa APC, rahoton Premium Times.

Bayan zaman masu ruwa da tsakin, ya bayyanawa manema labarai cewa mambobin APC sun shirya amsan gwamnan da mabiyansa.

Yace:

"Wannan zai karawa jam'iyyar mabiya nan gobe. Muna kyautata zaton cewa zuwansa zai amfanar da jam'iyyar a jihar. Saboda hakan muna masa maraba."
"Ba zamu yanke shawara kan komai ba tare da amincewar al'ummarmu ba, shiyasa muka gayyaci dukkan masu ruwa da tsaki. Ba zamu yarda da komai ba sai dai idan zai amfani jam'iyyar da jihar."
Daga cikin wadanda suka halarci zaman akwai tsohon gwamnan jihar, Alhaji Mamouda Shinkafi.

Shinkafi yace shigowar Matawalle jam'iyyar alkhairi ne ga al'ummar jihar, riwayar Daily Trust.

PDP Ta Ja Kunnen Gwamna Matawalle Kan Komawa APC
Gabanin shirin sauya shekar gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, daga jam'iyyar PDP, zuwa APC, babbar jam'iyyar adawar (PDP) ta gargadi gwamnan kan wannan matakin, tare da barazanar yin mai yiwuwa don kare dokokin jam'iyya.

PDP ta gargadi Bello Matawalle da ya sani cewa take-takensa sun yi daidai da shawarar barinsa kujerar mulki saboda an zabe shi a karkashin jam'iyyar PDP.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN