Da duminsa: Yansanda sun yi rugu rugu da yan bindiga a wani artabu, duba yadda ta faru


Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Benue ta tabbatar da cewa 'yan bindiga 14 sun mutu a yayin musayar wuta bayan wani yunkurin kai hari a wani ofishin 'yan sanda a garin Katsina-Ala, jihar Benue da safiyar Lahadi, The Nation ta ruwaito.

Mai magana da yawun ‘yan sanda DSP Kate Anene, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce a ranar Asabar, an kama wasu da ake zargin 'yan bindiga ne kuma an tsare su a ofishin ‘yan sanda da ke Katsina-Ala domin gudanar da bincike.

Amma ta ce a safiyar ranar Lahadi, da misalin karfe 1 na dare, wasu ‘yan bindiga, wadanda yawansu ya kai 50, sun kai wani mummunan hari a ofishin 'yan sanda a kokarin su na kubutar da wadanda ake zargin dake tsare.

Mai magana da yawun 'yan sandan ta ce jami'an sashin, wadanda tuni sun kasance cikin shirin ko ta kwana, sun yi artabu da 'yan bindigan tare da bindige 14 daga cikinsu a yayin musayar wuta yayin da wasu suka tsere da raunin harsasai da dama.

A rahoton Daily Nigerian, 'yan sanda sun shawarci jama'ar Katsina-Ala da su kwantar da hankulansu tare da bai wa 'yan sanda bayanai masu amfani.

Yadda 'Yan Bindiga Suka Yi Amfani da Motar Mahaifin Dalibi Wajen Sace Daliban Kebbi

A wani labarin, Rahotanni da Legit.ng Hausa ta samo sun bayyana cewa, 'yan bindigan da suka sace dalibai a jihar Kebbi sun yi amfani da motar wani mahaifin dalibi ne wajen sace daliban.

Idan baku manta ba, wasu mahara sun kai hari kwalejin gwamnatin tarayya dake garin Yauri a jihar Kebbi a ranar Alhamis kuma sun yi awon gaba da dalibai da ma’aikata, jaridar Guardian ta ruwaito.

Wani malami da bai so a ambaci sunansa ba ya shaida wa Daily Trust cewa kafin harin, sun samu labarin wani shiri na mamaye garin na Birnin Yauri.

Source: Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN