Da duminsa: Uwargida ta kashe Maigida, ta yanke mazakutarsa ta soya, duba abin da ya faru


Mahukunta sun kama wata mata bisa zargin kashe mijinta tare da yanke mazakutarsa kuma ta soya a kasar Brazil.

Yansanda sun kama Uwargida mai suna
Dayane Cristina Rodrigues Machado, yar shekara  33, a birnin Sao Goncalo ranar 7 ga watan Yuni.

Rahotanni sun ce matar ta kashe mijinta ne da karfe 4 na safe bayan zafafar muhawwara da suka yi domin kawo karshen aurensu na shekara 10.

Yansanda sun sami wuka a gefen gawar mijinta mai suna Andre kwance tsirara a tsakiyar daki. Ana kyautata zaton cewa ta yi amfani da wukar ne ta kashe Andre.

Wani abin mamaki shi ne yadda wannan mata ta yanke al'aurar Andre kuma har ta soya da man wake soya bisa dalili da ita kadai ta san manufar yin haka.

Ma'auratan suna da yara biyu kafin mutuwar mahaifin su Andre a hannun mahaifiyarsu.


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN