Da duminsa: Najeriya za ta buga wa kasar Gambia Kudade, ba sauran kai wa Turai


Babban Bankin Najeriya (CBN) ya amince bisa ka'ida don buga kudin Dalasi na kasar Gambiya, Daily Trust ta ruwaito.

Legit ta tattaro cewa, Gwamnan Babban Bankin, Mista Godwin Emefiele, ya amince da shawarar buga kudin daga Gwamnan Babban Banki na kasar Gambiya, Mista Buah Saidy, wanda ya jagoranci wata tawaga da ta ziyarce shi a ranar Talata.

Mista Emefiele ya ce Najeriya na da karfin gaske a harkar buga kudi kamar yadda take bugawa tun a shekarun 1960 kuma “a shirye muke mu taimaka wajen buga kudinku. Za mu iya kasancewa araha sosai ta fuskar tsadancewa,” in ji shi.

Tun da farko Gwamnan Babban Bankin na Gambia ya ce kasarsa na fama da karancin kudi sosai kuma suna son koyon yadda za su sarrafa kudinsu da suke bukata duk shekara suna masu jinjina tarin ilimi da gogewar Najeriya.

Ya ce a halin yanzu, sun bayar da umarnin a kwashe shekaru biyu ana harkar buga musu kudaden a kasashen waje amma suna duba yiwuwar yin hakan daga Najeriya idan Najeriya ta amince.

A nata bangaren, kamfanin buga kudi na Najeriya, Nigerian Security Printing and Minting Company Plc ya ce a shirye yake idan duk bangarorin biyu sun cimma matsaya.

EFCC Ta Bayyana Yadda Ake Sace Kudin Najeriya da Bitcoin, Ta Kwato Miliyoyi

A wani rahoton na daban, Shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya ce hukumar ta kwato kimanin dala miliyan 20 da barayi a yanar gizo suka wawure.

Mista Bawa, ya bayyana haka ne yayin shirin ‘Sunrise Daily’ na Channels Tv, ya kara da cewa an adana kudaden a cikin asusun yanar gizo na hukumar EFCC, Punch ta ruwaito.

Babban Bankin Najeriya a watan Fabrairun 2021 ya umarci bankuna da sauran cibiyoyin kudi su gano mutane da kungiyoyin da ke musayar kudin Intanet tare da rufe dukkan wadannan asusun.

Hakanan ya bayyana cewa ma'amala da musayar kudade da biyan kudi ta hanyar kudaden intanet haramun ne a kasar.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN