Da duminsa: Gwamnan Bauchi, Bala ya kori duka Kwamishinoni da masu bada shawara


A safiyar yau ne Gwamnatin jihar Bauchi ta fitar da sanarwar sallamar kusan daukacin kwamishinoni da masu ba gwamna Bala Mohammed shawara.

Kamar yadda sanarwar da ta fito daga ofishin mai taimaka wa gwamnan jihar Bauchi wajen yada labarai da hulda da jama’a, wasu hadimai hudu kacal suka tsira.

“Mai girma gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala A. Mohammed CON (Kauran Bauchi) ya amince da ruguza daukacin majalisar zartarwa da sauran masu mukamin siyasa.”

Daga ciki har da sakataren gwamnatin jihar (SSG), da shugaban ma’aikatan gidan gwamnati da dukkanin masu bada shawarwari na musamman face wadannan:

1. Mai bada shawara a kan harkar tsaro

2. Mai bada shawara a kan aiki da majalisar dokoki da tarayya

3. Mai bada shawara a kan inganta rayuwar jama’a

4. Mai bada shawara a kan yada labarai da hulda da jama’a

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN