Da duminsa: Bayan Twitter, Facebook ta goge tsokacin Buhari kan yakin basasa da ya janyo cece-kuce


Facebook, wata kafar sada zumuntar zamani ta cire tsokacin shugaban kasa Muhammadu Buhari a shafinsa.

Shugaban kasan a ranar Talata yayi barazanar maganin masu kai farmaki ofisoshin hukumar zabe mai zaman kanta kamar yadda sojoji suka yi wa 'yan tawaye a yakin basasa.

Buhari, soja mai mukamin janar amma wanda yayi ritaya ya yi yakin basasa wanda ya lamushe rayukan sama da mutum miliyan daya, Premium Times ta ruwaito.

"Da yawa daga cikin wadanda ke rashin da'a a yau yara ne da basu san barnar kadarori da rayukan da aka yi ba yayin yakin basasa. Mu da muka yi watanni 30 a filin daga, muka ga yakin basasa, zamu yi muku magana a yaren da kuke fahimta," yace.

Amma a ranar Juma'a, bayan rahoton da ma'abota Facebook suka dinga kaiwa, Facebook ta cire wallafar daga kafar.

"Duba da dokokinmu na duniya, mun cire wallafar da shugaban kasa Buhari yayi a shafinsa na Facebook bayan karya dokokinmu na hana tada tarzoma. Muna cire duk wata wallafa ta mutum ko kungiya da ta take dokokin Facebook," kafar tace.

Duk da a halin yanzu babu wallafar a shafin Buhari, har yanzu yana nan a na hadiminsa Femi Adesina.

Har yanzu babu tabbacin cewa gwamnatin Najeriya za ta dakatar da aiki da Facebook kamar yadda tayi da Twitter a yau.

A wani labari na daban, an tabbatar da kisan 'yan bindiga biyar a yammacin Laraba yayin da suka yi arangama da rundunar 'yan sanda a karamar hukumar Kurfi ta jihar Katsina.

Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan bindigan da zasu kai dari da hamsin sun tsinkayi kauyukan Wurma da Yarbudu, jaridar ThisDayLive ta ruwaito.

Amma kuma 'yan sandan dake kauyen Wurma sun yi gaba da gaba da 'yan bindigan. Majiya daga rundunar 'yan sandan tace daya daga cikin 'yan bindigan ya sheka lahira.

Source: Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN