Banbanci ya kare: Majalisa ta amince da daidaita Kwalin HND da na Digiri


Majalisar Dattawa ta amince da dokar da ta haramta nuna bambanci tsakanin babbar difiloma ta HND da kuma digiri na farko.

Lamarin ya biyo bayan kammala duba dokar a karo na uku da majalisar ta yi a yau Laraba, wanda kuma nan take ta amince da shi.

Sanata Ibrahim Shekarau daga Jihar Kano ne ya gabatar da rahoton kwamatin makarantun gaba da sakandare a zauren majalisar wanda ya duba Kudirin dokar mai suna 'Prohibition of Discrimination between First Degrees and Higher National Diplomas Bill, 2021 (SB.297)'.

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya ce batun nuna bambanci tsakanin babbar difilomar da kuma digiri ya fi shekara 15 a gaban majalisar.

"Wannan batun ya dade a gaban 'yan majalisa. Ina iya tunawa a Majalisar Wakilai ta 2003 zuwa 2007, wannan batun na cikin mafiya muhimmanci kuma wannan abin karfafa ne ga ɗaliban kwalejin fasaha (Polytechnic)," in ji shi.

Wannan na nufin kenan, daga yanzu babu bambanci tsakanin wadanda suka yi digiri a jami'a da kuma wadanda suka yi HND a kwalejin fasaha.

Sannan Ahmad Lawan ya roki gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kansu da su yi kokarin dabbaka sabuwar dokar.

"[Kuma] Ina rokon Gwamnatin Tarayya da dukkanin hukumomin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu su fara aiwatar da wannan a lokacin da Shugaban kasa zai amince da wannan kudirin."

A wani labarin, Shugaban majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila ya ce kundin tsarin mulkin kasar na 1999 ya gaza magance wasu manyan matsaloli da ke addabar kasar, abin da ya sa kenan 'yan majalisa suka yanke shawarin sauya shi, BBC Hausa ta ruwaito.

Gbajabiamila ya fadi hakan ne a wajen taron jin ra'ayoyin jama'a kan sauya kundin tsarin mulkin a Legas a ranar Talata, kamar yadda wata sanarwa da mai bai wa majalisar wakilan shawara kan yada labarai ta fitar.

Shugaban majalisar ya ce kundin tsarin mulki ba wai tushen kasa ba ne kawai, kamata ya yi ya zayyana ka'idojin zaman kasa da kuma burikanta na akida da gaskiya, amma "namu kundin tsarin mulkin na cike da nakasu," a cewar Gbajabiamila.

Source: Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN