An kama Ma’aikacin NDLEA a cikin masu laifin saidawa mutane miyagun kwayoyi


Hukumar NDLEA da ke da alhakin cafke masu safarar miyagun kwayoyi ta yi ram da wani daga cikin jami’inta mai-ci, a cikin wadanda ke harkar mugayen kwayoyi. 


This Day ta rahoto cewa an damke wannan ma’aikaci na hukumar da laifin saida miyagun kwayoyi ga wasu daliban jami’ar tarayya da ‘yan iskan gari a Ogun. Jaridar ta ce darektan yada labarai da wayar da kai na hukumar ta kasa, Femi Babafemi, ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar wa manema labarai a Abuja. 

Da yake jawabi a ranar Lahadi, Femi Babafemi, ya shaida wa ‘yan jarida an yi ram da mai taimaka wa mutanen da kwayoyi ne a ranar Laraba, 15 ga watan Yuni, 2021. 

Today ng ta ce hakan ya biyo bayan tsawon lokaci da aka dauka ana sa ido a kan matar wannan Bawan Allah, inda ake amfani da shagonta wajen yin aika-aikar. Yadda lamarin ya faru - Jami'in NDLEA Babafemi ya ce jami’an NDLEA sun yi ta bin wani ‘dan acaba da yaje shagon mai dakin wannan mutumi a garin Abeokuta, aka kama shi ya saye 1.17gm na kwaya. 

“Wannan kafin a cafke asalin wanda ake zargi, wani wanda hukuma ta dade ta na nemansa, sai aka yi ram da shi dauke da miyagun kwayoyi.” Inji Femi Babafemi. 

Jami'an NDLEA a bakin aiki Hoto: www.guardian.ng Source: UGC “Daga cikin abubuwan da aka kama shi da su akwai kwalabe 17, giram 22.26 na Codeine; kwayoyi 230 na tramadol; kwayoyi 61 flunitrazepam da giram 48.16 na moli.” 

Hukumar ta cigaba: “Bayan an cafke mutane biyu da ake zargi, sai wasu shugabannin kungiyar ‘daliban jami’a su ka tare ma’aikatan NDLEA da motar aikinsu.” Bayan sa’o’i ana takkadama, ma’aikatan NDLEA sun yi nasarar kama wanda ake zargi zuwa inda ake tsare shi, sannan an kama wani mai saida kwayoyi a garin Ilorin.

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN