Abdullahi Umar Ganduje: Ƴan bindiga ba su yi sansani a Dajin Falgore na Kano ba


Gwamnan Jihar Kano da ke arewacin Najeriya Abdullahi Umar Ganduje ya ce babu wasu ƴan bindiga da suka yada sansani a Dajin Falgore, kamar yadda wasu daga cikin kafafen yaɗa labaran ƙasar ke cewa.

Gwamna Ganduje ya faɗi hakan ne a wata hira da BBC bayan ganawa da manema labara, inda ya ƙara da cewa gwamnatinsa na aiki tare da hukumomin tsaro wajen ganin an ƙara inganta tsaro a faɗin jihar.

Ya ce suna aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnonin jihohin Bauchi da Kaduna kan matsalar tsaro, tare da ganin ƴan bindiga ba su kwararo zuwa jihohin ba.

Gwamnan ya ce matsalar rashin tsaro babban al'amari ne a Najeriya baki ɗaya, "har ta kai aka sauya baki daya shugabannin tsaro, sabbin kuma sun sha alwashin yin aiki tuƙuru," a cewarsa.

"Sannan ga wani sabon al'amari mai kyau na sa al'umma a cikin harkokin tsaro wato Community Policing.

"Muna fatan harkar tsaro za ta zama ta kowa da kowa. Kuma kamar yadda gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi suka yi alƙawari za a shawo kan matsalar muna fatan hakan ta kasance.

Sai dai saɓanin yadda wasu kafafen yada labaran kasar suka ruwaito cewar akwai ƴan bindiga da suka yi sansani a Dajin Falgore, ya ce ko kaɗan bai yi wannan furuci ba.

"Yan jarida ba su ba da rahoto daidai kan maganar da muka yi ba. Abin da ya faru shi ne a lokacin da aka far wa Dajin Sambisa, na gaya wa Shugaba Buhari cewa na yi hasashe idan aka tarwatsa su a can, to za su shigo sauran dazuzzukan Najeriya su zauna.

"Mu kuma a jihar Kano muna da babban Dajin Falgore, saboda haka ina so ya ba ni dama mu yi sansanin horar da sojoji a cikinsa.

"Mun kashe biliyoyi a cikin wannan daji a yanzu haka akwai gine-gine da yawa, kuma sojoji sun fara horar da ƙananan sojoji aikin harbi na soja.

"Don haka abin da ya kai ni Abuja don na faɗi abin da aka yi ne da kuma dalilin da ya sa aka yi," kamar yadda ya ce.

Wannan layi ne

Wasu labaran da za ku so

Wannan layi ne
Dajin Falgore, inda masu satar shanu ke addabar makiyaya
Bayanan hoto,

Gwamna Ganduje ya ce yanzu haka akwai sojoji na ba da horo a Dajin Falgore

Gwamnan ya ce yana ƙoƙari don ganin al'amuran tsaro ba su ɓaci a Kano kamar sauran jihohi ba.

"Mun haɗa ƙarfi da ƙarfe tskaanimu da jihar Kaduna da jihar Bauchi inda jami'an tsaronmu na zagayawa a ciki.

"A yanzu haka babu waɗansu ƴan ta'adda a cikin wannan daji, ko ta ka ji yadda lamarin yake kenan," a cewar Gwamna Ganduje.

A baya-bayan nan dai an sami ayyukan ƴan bindiga a Kano da sace mutane a wasu daga cikin ƙananan hukumomi a Kano.

Rahotun BBC

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN