Yanzu yanzu: Shugaban sojin Najeriya Janar Attahiru ya mutu a hatsarin jirgin sama


Shugaban rundunar sojin Najeriya Janar Ibrahim Attahiru ya rasu a wani hatsarin jirgin sama. Jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Akwai bayanai mabanbanta da juna kan dalilin hatsarin jirgin saman da ya rutsa da Janar Attahiru. Sai dai wata majiya ta soji ta shaida wa Jaridar Daily Trust cewa hatsarin ya faru ne a Kaduna ranar Juma'a.

Jaridar Thenation ta ce Janar Ibrahim ya rasu tare da mai dakinsa da wasu Hadimansa da ba a tantance ba kawo yanzu. Kuma ya je Kaduna ne domin Kaddamar da wasu ayyuka. Rahotanni sun ce jirgin ya Sami hatsari ne a filin sauka da tashinn Jiragen sama na Kaduna.

A sanarwar da rundunar sojin sama ta Najeriya ta fitar, ta tabbatar cewa lallai hatsari ya rutsa da wani jirgin samanta a Kaduna. Sai dai bata yi karin haske ba.

Karin bayani na nan tafe...


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN