Yajin Aiki: Gwamna El-Rufai Ya Gaza Kama Wabba a Kaduna


Kimanin awanni biyu bayan Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya ayyana shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa, NLC, Kwamared Ayuba Wabba da wasu a matsayin wadanda ake nema ruwa a jallo, gwamnan ya matsa kilomita 100 kusa da inda masu zanga-zangan suke.

Wabba da sauran shugabannin kungiyar suna jagorantar dubban masu zanga-zangar ne zuwa gidan Sir Kashim Ibrahim, sai tawagar motoccin gwamnan suka wuce su kusa da shatale-talen NEPA da ke babban birnin jihar na Kaduna, Daily Trust ta ruwaito.

Babu yadda za a yi gwamnan bai ga masu zanga-zangar ba da ke kan titi da ya bi a lokacin da zai tafi hedkwatar kamfanin rarraba wutar lantarki ta Kaduna, KEDCO.

Kamfanin ya nan kimanin kilomita 100 daga shataletalen NEPA a inda masu zanga-zangan suka taru.

An yi gaggawar bude kofar kamfanin a lokacin da tawagar gwamnan ta shiga.

Tawagar na gwamna El-Rufai ta fito daga harabar ta KEDCO kimanin mintuna 10 bayan shiganta.

Ma'aikatan lantarkin na daga cikin wadanda suka shiga yajin aikin da aka yi a jihar ta ta gurguntar da harkoki a Kaduna.

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Raya Birnin Tarayya Abuja, FCTA, ta rushe wani tashar tasi a NICON Junction, Maitama, Abuja, kan zargin mayar da tashar matattarar yan kwaya da bata gari, Daily Trust ta ruwaito.

Direktan (FCTA), sashin tsaro, Adamu Gwari, wanda ya yi magana yayin rushe tashar ya ce tashar barazanar tsaro ne sannan barazana ne ga muhallin mutanen da ke zaune a birnin. An Rushe Tashar Motar Saboda Ta Zama 'Matattarar Ƴan Ƙwaya' a Abuja.

Ya kuma ce rushe tashar mataki ne da aka dauka duba da irin kallubalen tsaron da ake fuskanta a jihar.

Source: Legit.ng


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN