Yadda ISWAP Ta Yi Amfani da Mata da Yara Wajen Hallaka Shekau


Mata da yara masu kananan shekaru na daga cikin mayakan da suka yi artabu da Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram, a daya daga cikin fadace-fadace mafi muni da yayi a rayuwarsa.

Wasu majiyoyi game da harin sun shaida wa Daily Trust cewa ISWAP ta yi amfani da mayaka 'yan tsakanin shekara 12 zuwa 30 a harin.

An ce duka bangarorin sun yi asara a artabun amma sansanin na Shekau ya fi yin asara yayin da shugaban ya yi kunar bakin wake ya kashe kansa ko kuma ya samu munanan raunuka da suka sa da wuya ya rayu.

Sai dai, Rundunar sojin Najeriya ta ce har yanzu ba ta samu labarin mutuwar shugaban kungiyar ta Boko Haram, Abubakar Shekau ba, Reuben Abati ya ruwaito.

An ce an horar da mayakan na ISWAP a Libya, Somalia da sauran kasashen waje.

An ce sun shirya sosai don auka wa shugaban na Boko Haram da ya share shekaru yana addabar al'ummar arewa maso gabashin Najeriya.

"Su (mayakan) hakika 'ya'yan wasu 'yan kungiyar ISWAP ne da aka kashe a wani lokaci," in ji daya daga cikin majiyoyin.

“Wasu kuma matasa ne da aka samo su a yayin samame a tsibirai da yawa da ke kewayen Tafkin Chadi.

"Kungiyar ISWAP ta zabi matasan cikin ruwan hankali. Don haka ya kasance mafi sauki a daukarsu yayin da wasu daga cikin matasan suka yarda suka shiga kungiyar wasu kuma da karfi aka tilasta su.

“Wasu daga cikinsu an haife su ne a lokacin yakin wasu kuma kanana ne lokacin da iyayen su suka shiga kungiyar a wajajen 2002. Bayan iyayensu sun mutu saboda rashin lafiya ko kuma arangama da sojojin Najeriya, yaran sun shiga tafiyar.

"Lokacin da kungiyar ta rabu biyu a 2016 , wadanda suka kaura da kansu ko kuma aka tilasta masu da karfi zuwa gabar tafkin Chadi a karkashin inuwar ISWAP sun goge a fagen horo saboda an dauke su zuwa Libya don samun horo kan yakar kungiyoyin asiri da sauran dabaru.

“An tura wasu zuwa kasashen Syria da Somalia… An kai su kasashen waje da yawa don samun horo. Saboda haka, wadanda suka dawo musamman tsakanin Maris zuwa Afrilu na wannan shekara sun taka rawa wajen tunkarar Shekau a cikin kwanakin da suka gabata.

"Sun kaddamar da mummunan farmaki tare da sauran manyan kwamandoji da mayakan da ke kasa kuma sun yi nasarar karbe iko.

Wata majiyar kuma ta ce an horar da wasu daga cikin matasa 300 din a matsayin "Likitocin kiwon lafiya, da masu ba da agajin gaggawa, da injiniyoyi, da kwararru a fannin IT, da kwararrun kan bam da kuma kanikanci."

Ya kara da cewa daga cikinsu akwai mata "wadanda ke aikin jinya da masu dafa abinci yayin da wasu kuma ke da kwarewar sarrafa bindiga, ma'ana za su iya shiga cikin yaki."

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE