Waiwaye: Hoton Shugaba Buhari yana rawa da wata mace ya haifar da cece kuce


Wani tsohon hoto na Shugaba Buhari yana more rayuwa lokacin da yake matashi ya haifar da zazzafan martani a shafukan sada zumunta.

Wani ma’abocin amfani da Facebook mai suna Ayo Ojeniyi ya dimauta yanar gizo da wani hoto wanda ba kasafai ake gani ba na Shugaba Buhari yayin da wani saurayi yake rawa da wata farar mace ba takalmi.

Da yake wallafa hoton, ya rubuta cewa:P

PMBya kasance dan sharholiya sosai yayin da yake tasowa. A zamanin nan, ya kame kansa !!! Dube shi yana shanawa a wani liyafa lokacin da yake saurayi !!!!

Buhari ya kasance dauke da murmushi yayin da suke rawa inda sauran matan da ke wurin suke kallo.

Dubi wallafar da yayi a ƙasa:

Mutane da yawa sun nuna farin ciki yayin da suke tsammanin cewa shugaban kasar ya fi shanawa a zamanin da yake tasowa idan aka kwatanta da yanzu.

Wasu suna mamakin dalilin da yasa suka kasance ba tare da takalmi ba.

Ayoola Akinkumi Olamide ya rubuta: M

Maishanawa? 1 daga cikin 50. Bayan barinsa mulki a 1985 sau nawa ya yi mu'amala da mutane a wajen Arewarsa. Lokaci guda da ya ziyarci Kudu maso Yamma shi ne lokacin da ya zo don karbar cin mutunci daga Lam Adesina. Wanene abokinsa na kut da kut a Kudancin kasar gaba daya kafin 2007? Ba komai ba ne shi face kifin rijiya har zuwa lokacin.

Adams Yusuf ya ce:K

Kazama mai tawali'u da kuma nutsuwa a lokacin da kake tsufa.K

Kumafa sauran kyawawan matan suna jiransa ya yi rawa tare da su. Lallai ma.

Segun Fagbemi ya ce:

Da ya ci gaba da ritaya.

Damuwar Najeriya ta yau ta wuce karfi da kuzarinsa.

A wani labarin, a ranar Laraba, 28 ga watan Mayu, 2021, tsohon gwamnan jihar Ogun, Cif Olusegun Osoba, ya caccaki hadimin shugaban kasa, Malam Garba Shehu.

Olusegun Osoba ya ja-kunnen mai magana a madadin shugaban Najeriyar ya bi sannu a hankali ka da jawabinsa ya rika sha ban-bam da na mai gidansa.

Jagoran na APC ya gargadi Garba Shehu a kan yin kalaman da suka bambanta da ra’ayin mai girma Muhammadu Buhari da matsayar jam’iyyar APC.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN