Rashin tsaro: Sultan yayi muhimmin kira ga Shugaban Buhari da Gwamnoni


Sarkin Musulmi, Sultan Alhaji Sa'ad Abubakar III ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni da su kawo karshen rashin tsaro a kasar nan, Jaridar The Nation ta wallafa.

Sarkin Musulmin wanda shine shugaban majalisar koli ta al'amuran addinin Musulunci a Najeriya, yayi wannan jawabin ne a Sokoto bayan sallar idin karamar sallah da aka yi a ranar Alhamis da ta gabata.

Ya ce: "Muna kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da dukkan gwamnonin jihohi da su gaggauta kawo karshen rashin tsaro da ya addabi kasar nan.

"A matsayinku na shugabanni, dole ne ku dage wurin sauke nauyin dake kanku na bada kariya ga al'umma.

"A don haka, dole ne ku kare zagewa wurin ganin kun dawo da zaman lafiya a kasar nan irin wanda muka dade da sanin muna da shi."

Sarkin Musulmin yayi kira ga Musulmi da su cigaba da yi wa shugabanninsu addu'a domin Allah ya basu damar daukar dawainiyar da ta hau kansu.

Yayi kira ga Musulmi da su cigaba da bayyana halayyar karamci da kaunar juna wanda sallah ke nunawa.

"Yau babbar rana ce garemu ta murna, ku nuna osyayya, kauna, goyon baya kuma a yi mu'amala mai kyau."

A wani labari na daban, a kalla 'yan sanda hudu ne ke tsaron gidan Maikano Abdullahi, jami'in fadar shugaban kasa wanda wasu barayi suka yi yunkurin shiga gidansa.

An gano cewa jami'an tsaro biyu ke aiki a lokaci daya, rana biyu, dare biyu a gidan, jaridar The Punch ta ruwaito.

Gidan yana da kusanci da gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ke da kusancin mitoci kadan da wani wurin da sojoji hudu ke zama.

Source: Legit.ng


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN