Mutanen Gari Sun Ƙona Ƴan Bindiga Uku Ciki Har da Mace a Sokoto


Fusatattun matasa sun kashe wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a yayin da suka yi yunkurin kai hari a Goronyo a ranar Laraba, Daily Trust ta ruwaito.

Matasan sun kuma ƙona ofishin ƴan banga da aka fara ajiye wadanda ake zargin.

Yan bindigan sun zo wani Rugar Fulani da ke wajen Goronyo cikin dare domin su sace shanu amma mutanen suka yi fito-na-fito da su suka kama uku cikinsu.

"Mutanen a shirye suke. Harsashi baya ratsa su. Sun dakile harin kuma suka kama uku cikin yan bindigan suka mika su hannun ƴan banga da safe, in ji wani mazaunin garin.

"Da labarin ya isa wurin matasan mu, sun taru sun tafi ofishin ƴan banga da aka ajiye su a Goronyo.

"Kalaman da ke fitowa bakin ƴar bindigan ya fusata su inda ta ke cewa ba yau aka fara kamata ba kuma ta san za a sake ta.

"Wannan ne ya ɓata musu rai, suka fi karfin ƴan bangan suka cinnawa ofishin wuta.

"Daya daga cikin wanda ake zargin ya mutu a ofishin yan bangan, macen da ɗayan na mijin sunyi yunkurin tserewa amma aka kama su aka kashe su aka ƙona gawarsu," a cewar wani ganau.

Shugaban ƙaramar hukumar, Abdulwahab Yahya ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce jami'an tsaro suna sintiri domin tabbatar da doka da oda.

A cewarsa, ƴan bindiga sun dade suna sace shanu a yankin duk da jami'an ƴan sanda 60 da ke garin.

Kakakin ƴan sandan Sokoto, ASP Sanusi Abubakar shima ya tabbatar da afkuwar harin amma ya ce ba shi da cikakken bayani a lokacin haɗa wannan rahoton.

Source: Legit News


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN