Matsalolin Nijeriya: Abin Da Gwamnoni Za Su Yi Su Taimaki Buhari -Jonathan


Tsohon Shugaban Kasan Nijeriya Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana abin da ya kamata gwamnonin kasar su yi wajen taimaka wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari warware matsalolin da ke addabar kasar.

 

A cewar Goodluck Jonathan, Shugaba Muhammadu Buhari ba shi ne kashin bayan jan ragamar kasar ba, gwamnoni ne, kasancewar shi mutum daya ne kawai da yake Abuja idan aka yi la’akari da irin rawar da gwamnonin suke takawa wajen tafiyar da kasa.

 

Baya ga wannan, Jonathan ya bayyana Gwamnoni a matsayin kungiyar da ke gudanar da mulkin kasar a zahiri, yana mai cewa, domin da jihohi ‘Yan Nijeriya suka dogara ba bangaren tarayya ba.

 

Don haka Goodluck ya ce babban abin da gwamnonin za su yi su taimaka wa shugaban kasa wajen warware matsalar kasa shi ne su hadu a karkashin inuwar Kungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF), don tattaunawa kan batutuwan da za su kai ga cimma matsaya don samun mafita.

 

Tsohon shugaban wanda ake rade-radin cewa zai iya sake takarar Shugaban kasa, ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a Benin kwanan nan yayin bikin murnar cika shekaru 50 na Mista Charles Osazuwa, shugaban wata kungiyar Kiristoci da ake kira ‘Rock of Ages Christian Assembly’.

 

A cewar Jonathan, haduwar dukkan gwamnonin a kan turba daya don tattaunawa tare da samar da hanyoyin magance matsalolin da suka shafi Nijeriya zai taimaka wa Shugaban kasa wanda ya dogara da bayanai daga sassan jihohin.

 

Jonathan ya kara da cewe, ”Gwamnonin kansu ya kamata su ci gaba da ganawa, ba na kaunar yadda gwamnonin Arewa za su hadu su yi taro a shiyyarsu, bayan sun fitar da matsayinsu sai gwamnonin kudu su yi fatali da shi.

 

“Sannan gwamnonin kudu za su hadu su ma a shiyyarsu su yi taro, bayan sun ce ga matakan da suka yarda a dauka sai ka ji su ma gwamnonin Arewa sun yi watsi da abin, hakan ba zai taimaki kasarmu ba. Gwamnoni kamata ya yi su hadu a karkashin kungiyarsu, domin su mutanen da ke tafiyar da kasar nan ne, shugaban kasa mutum daya ne kawai da ke Abuja,” in ji shi.

 

Ya ci gaba da cewa, “Jihohi, musamman a kasar da kananan hukumomi ke da rauni sosai, su ne mutane ke jingina da su. Don haka idan gwamnonin jihohi suka hadu suka tattauna, suka yi gabatar da shawarwari kan abubuwan da suka dace da kasar nan, to za mu ci gaba.”

 

“Ban cika jin dadin ganin kiyayya tsakanin gwamnoni ba, ya kamata su hadu su tattauna da junan su,” in ji shi.

 

Ya ce, “idan akwai batutuwan da suka shafi jiha daya ko biyu, ina ganin ya kamata gwamnoni su taru su ga yadda za su hada kai su zo da hanyar magance wadannan matsalolin.”

 

Jonathan ya kuma bayyana cewa, tun yana kan mulki bai taba amfani da matsayinsa wajen gallaza wa mutane ba.

 

Tsohon Shugaban kasar ya ce, yayin da yake cikin siyasa, yana da yakinin ba zai taba musguna wa kowa ba.

 

“Imanina musamman lokacin da na shiga siyasa ba don amfani da damar ta wucin gadi ba ne, ina kallon matsayin da Allah ya ba ni ba mai dorewa ba ne, don haka ba zan yi amfani da shi in addabi kowa ba.”

 

“Wasu daga cikin abubuwan da na yi lokacin da nake mulki wanda har yanzu mutane ke tunawa tare da yabawa shi ne ban yi amfani da matsayina ba wajen kashe gallaza wa kowa. Duk wani mukamin da na samu ta hanyar taimakon Allah bai kamata na yi amfani da shi don haifar da wahala ga wasu mutane ba,” in ji shi.

Rahotun Jaridar Leadershipayau a Hausa.leadership.ng


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN