Manyan Sojoji sun fara rige-rige a kan wanda zai gaji kujerar Shugaban hafsun sojan kasa


An soma harin kujerar shugaban hafsun sojojin kasa a Najeriya, hakan na zuwa ne bayan mutuwar Laftanan-Janar Ibrahim Attahiru a ranar Juma’a.

Jaridar Daily Trust ta ce rade-radin da ke yawo na nada Manjo-Janar Danjuma Ali-Keffi a matsayin sabon hafsun sojan kasan Najeriya, ba gaskiya ba ne.

Asali ma akwai manyan sojojin kasa fiye da 30 a gaban Manjo-Janar Danjuma Ali-Keffi a yanzu.

Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta na cewa watakila Mai girma Muhammadu Buhari ya dauko sojan Ibo a matsayin sabon hafsun soja na kasa.

Shugaba Muhammadu Buhari zai yi hakan ne domin rufe-bakin masu kukan cewa ba a tafiya da jami’an yankin Kudu maso gabas wajen bada mukamai.

Masana suna ganin akwai bukatar a nada sabon hafsun saboda yakin da ake yi, amma jami’an tsaro suna ganin ya yi wuri da yawa a lokacin da suke makoki.

Wani masani a kan sha’anin tsaro, Kabiru Adamu, ya yi magana da ‘yan jarida, ya ce zai yi kyau shugaban kasa ya zabo kwararren sojan da ya san kan aiki.

Kabiru Adamu yake cewa abin da ya fi dacewa shi ne ayi watsi da batun kabilanci a gefe, a nemo jami’in da yake gogewa, kuma ya yi nisa a gidan sojan kasa.

Idan har shugaban kasa ya zakulo sabon hafsu daga kudu maso gabashin Najeriya, surutun da ake yi na cewa gwamnatin nan mai-ci ta ware Ibo, zai ragu.

Matsalolin tsaro uku ne suke fuskantar kasar nan a yau; ‘yan ta’addan da suke tada kafar baya, miyagun ‘yan bindiga da kuma masu rajin a barka Najeriya.

Wani mai magana a kan abin da ya shafi kasa, Malam Abdulhaleem Ishaq Ringim, ya ce da shi yake da wuka da nama, da Manjo-Janar Ben Ahanotu zai nada.

A cewarsa, Janar Ahanotu ne ya yi nasarar cafke shugaban Boko Haram na farko, Mohammed Yusufu a 2009, yanzu shi ne jami’in da ke shirya tsare-tsaren sojoji.

Ku na da labari cewa hadarin jirgin sama ne ya yi sanadiyyar mutuwar Laftana Janar Ibrahim Attahiru da wasu manyan jami'an sojojin kasa a makon jiya.

Babban sojan kasan ya cika ne kwanaki kadan da jin labarin mutuwar shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, wanda rikicin cikin-gida ya ci shi.

Source: Legit Nigeria

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN