Kasar Faransa za ta kawo wa Najeriya dauki domin shawo kan matsalar tsaro - Shugaban Faransa


Ƙasar Faransa tayi alÆ™awarin taimka wa Najeriya wajen magance matsalar tsaron dake addabarta, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Babban mai taimakawa shugaban ƙasa Buhari wajen yaɗa labarai, Malam Garba Shehu, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar.

Yace shugaba Buhari ya samu yardar shugaba Emmanuel Macron da gwamnatinsa a wajen taron Æ™asashen Africa dake gudana a Faransa, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

A jawabin, shugaba Macron yace gwamnatinsa na fatan taimakawa Najeriya da dukkan ƙarfinta domin kawo ƙarshen matsalar tsaron da ƙasar ke fama dashi.

Jawabin yace: "Yayin jawabinsa a wajen taron, shugaba Macron ya nuna goyon bayansa ga Najeriya da jama'ar dake cikinta bisa namijin ƙoƙarin da suke yi wajen kawo ƙarshen matsalar tsaron dake addabar su."

"Macron yace gwamnatinsa zata kawo ɗauki, zata yi amfani da duk ƙarfinta domin taimakawa ƙasar ta magance matsalar tsaron da yaƙi ci yaƙi cinyewa."

Shugaban Faranca ya ƙara da cewa gwamnatin sa zata taimakawa Najeriya wajen fuskantar ƙalubalen dake tattare da allurar rigakafin COVID19.

Shugaba Buhari ya tabbatar wa takwaransa na Faranca cewa Najeriya a shirye take tayi aiki tare da Faransa da sauran ƙasashen duniya domin tabbatar da an dawo da zaman lafiya a Najeriya.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Su Hallaka Sojoji Biyu, Sun Yi Awon Gaba da Wani ÆŠan China

Wasu yan bindiga sun kai sabon hari ƙauyen Nasko dake ƙaramar hukumar Magama a jihar Neja.

Jami'an soji sun maida martani ga yan bindigan inda akai É—auki ba daÉ—i a tsakaninsu, biyu daga cikin sojojin sun rasa rayuwarsu.

Source: Legit.ng


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN