Jirgin ruwa ya nutse da mutum 160 a jihar Kebbi, an ceto mutum 20 da gawa


Mutane da dama sun bace a jihar Kebbi bayan jirgin ruwa dauke da akalla mutane 160 ya kife a cikin ruwa a rafin Kwara ranar Laraba.

Wani jami'i a Ngaski mai suna Abdullahi Buhari Wara ya ce jirgin ya fito daga jihar Niger kuma yana kan hanyarsa ce ta zuwa jihar Kebbi. AFP ta ruwaito.

Ya ce "An fara aikin ceton wadanda suka nutse, amma mutum 22 ne aka ceto kawo yanzu, an kuma gano gawa guda daya. Yanzu haka bamu gan mutum 140 ba. 

Wara ya ta'allaka hatsarin da shake jirgin da aka yi da mutane fiye da kima. Ya ce mutum 80 ne ka'idar yawan mutanen da jirgin ya kamata ya dauka, amma ya dauko mutane 160 har da buhuhuwan kasa da aka debo na hakan zinari.

Rahotanni sun ce jirgin ya tsage ne a cikin ruwa yayin da yake cikin tafiya, sakamakon haka jama'a suka nutse a cikin ruwan.

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN